Shugaban kwamitin hukumomin tsaron cikin gida na majalisar tarayya, Honorable Abdullahi Aliyu ya ƙawata sabon Kwamandan rundunar tsaron NSCDC a Katsina da ya samu ƙarin girma
Honorable Abdullahi Aliyu ya ƙawata sabon Kwamandan rundunar tsaron NSCDC a Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Monday, 04 Nov, 2024
Shugaban kwamitin hukumomin tsaron cikin gida na majalisar tarayya, Honorable Abdullahi Aliyu ya ƙawata sabon Kwamandan rundunar tsaron NSCDC a Katsina da ya samu ƙarin girma.
Shugaban kwamitin harkokin tsaron cikin gida na Hon. Abdullahi Aliyu, Dujiman Katsina, ya ƙawata Babban Sufeto Jibril Usman, wanda ya samu karin girma a shekarar 2024 da sabon matsayi a ranar Litinin 4 ga Nuwamba, 2024 a Katsina.
A lokacin ƙawata shi, Hon Talban Musawa, ya samu goyon bayan kwamandan NSCDC na jihar Katsina, kwamandan Jamilu Abdu Indabawa, wanda ya samu wakilcin, ACC Aliyu Adamu Bakori.
Katsina Post ta samu cewa, mai Magana da yawun rundunar, SC Buhari Hamisu, shi ne ya sanar da haka ga Manema Labarai ɗauke da sanya hannun sa.
Da yake jawabi shugaban hukumar ya yaba da kyakykyawan jagoranci na haziki CG Ahmed Abubakar Audi PhD, mni, OFR, tare da sake fasalin hukumar ta yadda za ta yi aiki fiye da wanda take yi a baya.
A cewar sa, dole ne ya yaba da alkairai da salon jagorancin kwamandan Janar, musamman sabbin dabarunsa na kare muhimman ƙadarorin ƙasa, kayayyakin inganta rayuwar jami'an da kuma kawar da kasar daga wasu nau'o'in zagon kasa ga tattalin arzikin ƙasa. Haka kuma ya ya bawa kwamandan jihar bisa jajircewarsa na matakan inganta tsaro ga mutanen Katsina.
Shi ma, Dujiman Katsina ya taya Babban Kwamanda, wanda ya zama Kwamandan VIP na jiha saboda karin girma da ya samu zuwa mukamin Babban Sufeto (CSC). Ya bayyana cewa, girman da ya samu ya dace da shi duba da irin gudummawar da ya bayar da sadaukar da kai ga hidimtawa ƙasa.
Kazalika, ya ce Kwamandan ya yi ƙoƙarin sosai wajen daidaita ayyuka daban-daban da nufin magance matsalolin tsaro a jihar. Ya ce gudunmawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya da inganta tsaro a jihar suna da yawa.
Source: Katsina Post, Katsina News, Dikko Umaru Raɗɗa