Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Yin Sauƙi A Katsina
Jerin yadda farashin Abinci yake a jihar Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Tuesday, 05 Nov, 2024
Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Yin Sauƙi A Katsina
Ana ci gaba da samun saukin Farashin kayan abinci inda buhun Alabo ya dawo dubu 50,000 zuwa 60,000 a wasu kasuwannin jihar Katsina
Kasuwar garin Dutsi,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun Masara - 58,000 ja - 60,000
2- Buhun Dawa 'yar kudu - 68,000 Mori - 68,000 Fara - 53,000 ta - 79,000
3- Buhun Gero - 74,000
4- Buhun Gyadar kulli - 90,000 Mai bawo - 40,000
5- Buhun Kalwa Mai gari - 60,000 marar gari - 76,000
6- Buhun Alabo sabo - 50,000
Kasuwar garin 'Yantumaki a karamar hukumar Danmusa, ga yadda farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara - 58,000
2- Buhun Gero tsoho - 65,000 Dauro - 64,000
3- Buhun shinkafa tsaba - 120,000 shenshera - 50,000
4- Buhun Gyada - 128,000 Mai bawo - 42,000
5- Buhun Wake - 108,000
6- Buhun Waken suya - 48,000
7- Buhun Tattasai solo - 60,000
8- Buhun tumatur - 18,000
9- Buhun Albasa - 84,000
10- Buhun Ridi - 120,000
11- Buhun Dabino - 160,000
12- Buhun Alkama - 100,000
Kasuwar garin Dandume,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun masara Fara - 58,000 ja - 60,000
2- Buhun Dawa - 70,000
3- Buhun Gero - 67,000
4- Buhun Dauro - 80,000
5- Buhun shinkafa tsaba - 120,000 140,000 shenshera - 53,000 ta tuwo - 140,000
6- Buhun Gyadar kulli - 185,000 ja - 170,000
7- Buhun wake fari - 150,000
8- Buhun waken suya - 81,000 _ 82,000
9- Buhun Makani - 25,000
10- Buhun Alkama - 100,000
11- Buhun Barkono Dan minci - 250,000 Dan kuyalo - 350,000 Dan zamfara - 250,000
Kasuwar garin Charanchi, ga yadda Farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara - 62,000 zuwa 65,000
2- Buhun Dawa - 44,000_48,000
3- Buhun Gero - 64,000 zuwa 75,000
4- Buhun Shinkafa - 120,000 zuwa 140,000
5- Buhun Gyadar kulli - 130,000_140,000
6- Buhun Wake - 110,000_115,000
7- Buhun waken suya -84,000_88,000 durin gona
8- Buhun Alabo - 50,000_60,000
9- Buhun Garin kwaki - 59,000_60,000
Daga Aysha Abubakar Danmusa.