Gwamnatin Katsina Za Ta Tallafa Ma Mata Waɗanda Lalurar Shaye-shaye Ya Shafa
Gwamnatin Katsina za ta tallafa ma Mata waɗanda lalurar shaye-shaye ya shafa Kwamishiniyar harkokin
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Friday, 16 Feb, 2024
- Reporter : zaharaddeen Gandu
Gwamnatin Katsina za ta tallafa ma Mata waɗanda lalurar shaye-shaye ya shafa
Kwamishiniyar harkokin Mata ta jihar Katsina, Zainab Musa Musawa ta bayyana cewar Gwamnatin jihar Katsina za ta tallafa wa Mata da Matasa masu fama da lalurar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a musamman waɗanda Shaye-shayen ya illatasu a jihar.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, gwamnatin za ta taimaka wa masu shaye-shayen ta hanyar tattaunawa da su, da ba su dama da kuma ba su nau’ikan tallafi na zamantakewar rayuwa.
Tunda farko, kwamishinar ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa, gwamnati na haɗa kai da hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA wajen magance matsalar shan miyagun ƙwayoyi da Mata ke ta'ammali da su a jihar.
Zainab Musawa ta bayyana hakan a ranar Talata 13 ga watan Fabrairu na shekarar Dubu Biyu da Ashirin da Huɗu.
Ta ƙara da cewa, za su fara gangamin taron wayar da kai kan illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi musamman a ɓangaren Mata, tace ƙungiyoyi da yawa masu zaman kansu da ke fafutukar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi tuni suka nuna sha’awarsu ta haɗa kai da su a gangamin taron da suke shirin yi ba da jimawa ba.
Kwamishinar ta koka da yadda macen da ake sa ran za ta zama madubi kuma makaranta ga ‘ya’yanta, amma wasunsu su shiga munanan ɗabi’u da za a cin zarafin su, ko kuma su ɗauki ɗabi'ar safarar miyagun ƙwayoyi
da sauran abubuwan da za su iya lalata makomarsu.
Ta jaddada cewa, gwamnatin jihar Katsina za su ƙarfafa gwiwa, ta yadda idan suka koma ga iyalansu su tsunduma cikin harkokin kasuwanci na din-din-din.