Gwamna Raɗɗa ya nemi ɗauki daga hukumar samar da Abinci ta Duniya

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

FB_IMG_1709404006293_1

Gwamna Raɗɗa ya nemi ɗauki daga hukumar samar da Abinci ta Duniya 

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira da a kawo masa ɗauki cikin gaggawa kan matsalar tsaro da yayi silar ƙarancin Abinci da ta addabi yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi kwanan nan a Abuja tsakanin jami’an gwamnatin jihar Katsina da wakilan hukumar samar da Abinci ta Duniya (WFP), Malam Radda ya yi ƙarin haske kan yadda rikicin ya yi ƙamari wanda har aka samu yawaitar yunwa a yankunan.

Katsina Post ta samu cewa, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan jihar Katsina Ibrahim Kaula Mohammed, shi ya sanar da hakan a wata takardar da ya raba ma Manema Labarai ɗauke da sanya hannunsa a ranar 18 ga watan Mayu, 2024.

Da yake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tallafawa al’ummar jihar, Gwamna Radda ya bayyana matakan da suka ɗauka domin daƙile illolin ƙarancin Abinci a jihar.

Gwamna Radda ya godewa wakilan hukumar samar da Abinci ta Duniya (WFP) ƙarƙashin jagorancin daraktan ƙasar, David Stevenson, saboda amincewa da yankin Arewa maso Yamma a matsayin wani yanki mai mahimmanci da ke buƙatar taimako.

Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa tun da ta hau ofishin kusan shekara guda da ta wuce ya fara yunƙuri da yawa don yaƙi da rashin tsaro, amma halin da ake ciki yanzu akwai tarin ƙalubale a lamarin.

Gwamnan Katsina ya kuma yi nuni da mummunan tasirin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a jihohin Zamfara da ke makwabtaka da su. A yayin da yake bayyana halin da jihohin biyu ke ciki a matsayin abin ban tsoro, ya jaddada buƙatar samun goyon bayan ƙasa da ƙasa cikin gaggawa.