Soja Ya Harbe Abokin Aikin Sa Soja A Katsina
- Posted By: Sadiq Bindawa --
- Saturday, 26 Oct, 2024
Soja Ya Harbe Abokin Aikin Sa Soja A Katsina
Hukumar rundunar sojin Najeriya ta ce Cikin sojojin da aka tura FOB Dansadua na Operation FANSAN YAMMA, an samu rahoton cewa daya daga cikin su ya Bindige abokin aikin sa.
Direktan yada labarai hedikwatar tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 3 na safe a yankin Dansadau na jihar Katsina.
Buba ya ce jami’in da aka bayyana sunansa da Leading Seaman Akila A, an kama shi, kuma ana tsare shi domin aiwatar da bincike.
A cewarsa, bayan bincike, za a mayar da shari’ar zuwa kotun soji, wadda aka saba shirya domin magance irin wadannan munanan laifuka a tsakanin sojoji.
Yace har yanzu ba’a bayyana sunanan mamacin ba saboda wasu dalilai amman rundanar zata sanar da sunan shi nan bada jimawa ba.
“Saboda haka, muna jan kunne ga ‘yan jarida da su kula wajen fitar da rahoton sunan wanda aka kashe don gujewa dagawa yan uwan mamacin hankali” inji shi.