An kama Matashi da zargin yi ma Yarinya fyaɗe da jefa ta rijiya a Katsina

An yi ma Yarinya fyaɗe an jefa ta rijiya a Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

Rundunar Yansanda

An kama Matashi da zargin yi ma Yarinya fyaɗe da jefa ta rijiya a Katsina 

An kama wani matashi mai shekaru 24, mai suna Usman Mohammed Iyal, bisa zargin yi wa Yar shekara 16 Fyaɗe da yunkurin halaka ta ta hanyar jefa ta a cikin rijiya a cikin birnin Katsina.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 27 ga watan Satumba 2024 a yayin da mahaifiyarta ta aike ta a wani waje.

Kamar yadda Katsina Post ta samu daga LEADERSHIP cewa, an dakile yunkurin wanda ake zargin ne a yayin da 'yan sanda suka dau matakin gaggawa na bincike wanda ya kai ga ceto yarinyar daga rijiya.

Acewar rundunar  yansandan jihar Katsina,  wanda ake zargin, lokacin da yake yunkurin yi ma yarinyar fyaɗe, ya yi wa yarinyar barazana da wuƙa tare da kai ta wani kango domin aikata abinda yake da burin yi da ita.

Inda ake zargin bayan ya gama yi mata fyaɗe, ya kuma jefa yarinyar cikin rijiya bisa niyyar halaka ta.

Tunda farko, Mahaifin yarinyar, Abdullahi Sabitu, shi ne ya kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin 'yansanda a jihar Katsina, inda a lokacin 'yansanda suka yi nasarar ceto yarinyar daga rijiyar tare da kama wanda ake zargin. 

Yarinyar dai na ci gaba da karɓar kulawar likitoci a jihar, haka kuma rundunar 'yansandan ta ce ana ci gaba da bincike.