Jami'an tsaro sun daƙile wani harin 'Yanbindiga na ramuwar-gayya a Danmusa

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

undefined

Jami'an tsaro sun daƙile wani harin 'Yanbindiga na ramuwar-gayya a Danmusa

Wasu 'Yanbindiga ɗauke da muggan makamai da ba a san adadinsu ba sun yi yunƙurin shiga garin Danmusa domin kai wani harin ramuwar-gayya da suka shirya kaiwa a garin

Tun asali majiyar ta tabbatar da cewar 'yan bindigar sun ta shi da zummar kai ramuwar gayya a garin Danmusa. Amma jami'an tsaro suka sake samun nasarar fatattakarsu.

Majiyar da Katsina Post ta samu shi ne, sun yi yunƙurin kai harin ne a hedikwatar ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina cikin daren Litinin 29 ga watan Afrilu 2024.

Sai dai bayanan da DCL Hausa suka samu, sun ce jami'an sun yi nasarar daƙile wannan yunkuri hari da aka kira na ramuwar gayya. Yunkurin 'yan bindigar ya biyo bayan wani aikin fatattakar 'yan bindiga da jami'an tsaro aka sanar cewa sun yi a Ƙauyen Katsira, inda bayanai suka ce jamian tsaro sun yi nasarar konawa tare da lalata mafakar 'ya bindigar da dama.

Har lokacin haɗa wannan rahoton, bayan samamen da jami'an tsaron suka kai ma 'yan ta'addan, babu wani rahoto da aka samu na kashe ɓangarorin biyu walau jami'an tsaro ko 'Yanbindiga ko jikkata wasunsu ba, amma wata majiya daga jami'an tsaro da ta nemi da a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa an yi wa 'yan bindigar ɓarna mai tarin yawa.