'Yanbindiga sun kashe ɗiyar Kansila, sun yi garkuwa da Dagaci a jihar Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

IMG-20240405-WA0086

'Yanbindiga sun kashe ɗiyar Kansila, sun yi garkuwa da Dagaci a jihar Katsina

Wani mummunan harin da ƴan ta’adda suka kai a ƙauyen Tuge da ke gundumar Tuge a ƙaramar hukumar Musawa a jihar Katsina, ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane 3 da ba su ji ba ba su gani ba, da suka haɗa da maza biyu da ɗiyar kansilan Tuge, tare da yin garkuwa da mutane biyu a ciki har da dagacin ƙauyen, Kabir Hussaini.

Lamarin ya faru a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu, 2024, da misalin ƙarfe 12:00 na dare, sakataren ƙaramar hukumar, Hon.  Ahmad Surajo, ya tabbatar wa da jaridar Hausa Daily Post cikakken bayanin harin, inda ya bayyana matukar kaɗuwa da ɓarnar da ta'addancin ya haifar.

Surajo, ya bayyana cewa ƴan bindigar ba wai kawai sun yi garkuwa da dagacin ƙauyen da wani mutum guda ba, sun kuma kashe wasu mutane uku da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da ɗiyar Hon. Hussaini Ibrahim wanda shi ne kansilan da ke wakiltar gundumar Tuge.

A cewar wata majiya, mazauna ƙauyen sun yi yunƙurin neman agajin gaggawa ta hanyar kiran jami’an tsaro a lokacin harin, amma babu wani taimako da suka samu har sai bayan ‘yan ta’addan sun bar yankin.  "Sai dai kuma jami’an ƴan banga da Community Watch Corps sun isa ƙauyen cikin gaggawa bayan ƴan bindigar sun gudu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya yi wa jaridar Hausa Daily Post ƙarin bayani, inda ya bayyana cewa, dandazon ƴan bindiga ne suka kai hari a ƙauyen da misalin karfe 10:00 na dare, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku, da yin garkuwa da wasu biyu, da kuma  barnar dukiya da suka haɗa da gida da shaguna biyu.

Aliyu ya jaddada cewa ana ci gaba da kokarin ganin an ƙara kaimi wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su tare da kamo wadanda suka aikata wannan ɗanyen aikin.

Al’ummar yankin dai na cikin ruɗanin mummunar illar da wannan rikici ya haifar, kuma hukumomi na aiki tukuru domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.