Jami’an tsaro sun ceto wasu Fasinjoji 17 da aka yi garkuwa da su a Katsina
Rundunar tsaro ta haɗin gwiwa ta kuɓutar da wasu fasinjoji 17 da aka sace waɗanda galibinsu Maza ne daga hannun ‘yan ta’adda a yankin ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.
A Wata majiyar da Katsina Post ta samu daga Channels ta ce, nasarar ta biyo bayan wani kiraye-kirayen da aka yi a ranar 11 ga Mayu, 2024, inda rundunar sojin suka shiga dajin.
An ce, a lokacin shiga dajin har da rundunar sojojin Najeriya ta 9 tare da haɗin guiwar rundunar ‘yan sandan Katsina, da jami’an tsaro na al’umma na jiha, mafarauta na musamman, da mafarauta na garin Batsari, a dalilin haka kuma cikin gaggawa aka tura su wurin kuma akai nasara.
Majiyar ta ce, da isar jami’an tsaro na hadin guiwa sun yi artabu da ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su, inda suka gudu suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su, suka tsere zuwa cikin wani dajin da ke kusa da wurin.
Majiyar sojojin ta bayyana cewa an yi nasarar ceto dukkan fasinjojin da aka sace kuma an sako su ga jami’an karamar hukumar Batsari da ke jihar.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya bayyana cewa, sojojin na ci gaba da aiki tuƙuru a yankin na jihar Katsina domin daƙile ci gaba da aikata miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron mazauna yankin da suke fama da Iftila'in matsalar tsaro.