Yadda Aka Gudanar Da Muhawara Da 'yan Takarar Gwamnoni 4 A Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Tuesday, 24 Jan, 2023
- Reporter : zaharaddeen Gandu
Yadda aka gudanar da Muhawara da 'yan takarar gwamnoni 4 a Katsina
An gudanar da Muhawara tsakanin 'yan takarar gwamnoni 4 dake neman jagorancin gwamnatin jihar Katsina.
Muhawarar ta kasance a babban filin taro na Local Government Service Commission a cikin birnin Katsina.
Daga cikin 'yan takarar masu son jagorancin gwamnatin jihar Katsina, sun haɗa da; Dakta Dikko Umar Raɗɗa a jam'iyyar APC, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke a jam'iyyar PDP, Imrana Jino a jam'iyyar PRP, sai kuma Injiniya Nura Khalil a tutar jam'iyyar NNPP.
Katsina Post ta rawaito cewa, BBC Hausa ta shirya Muhawarar ne domin 'yan takarar su fiddo manyan ƙudirorinsu na yadda za su ciyar da jihar Katsina gaba idan ɗaya daga cikin su ya zama gwamnan Katsina.
An fara gudanar da Muhawarar ne da misalin ƙarfe 10:15 na safe, inda aka kammala taron da misalin ƙarfe 12:04 na rana.
A yayin aiwatar da Muhawarar, an ba ma al'umma damar yi ma 'yan takar tambayoyi tare da jin amsoshi daga bakunan 'yan takarar.
Kamar yadda aka fara taron lafiya haka aka gama shi lafiya, Katsina Post ta rawaito cewa, babu wanda aka ci mutuncin sa ko cin zarafin sa a yayin gudanar da Muhawarar.