Latest News

Za'a Daga Darajar Cibiyar Kula Da Lafiya Ta Garin Faskari Zuwa Babbar Asibiti

Za'a daga darajar cibiyar kula da lafiya ta garin Faskari zuwa babbar asibiti Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta jihar Katsina ta ce zata daga daga darajar dakin shan magani na garin Faskari zuwa babbar asibiti. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Bishir Gambo Saulawa ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati jin kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa a ranar Laraba. A cewar sa, majalisar zartarwar ta amince da a ware a kuma kashe kusan Naira miliyan 600 wajen yin wannan aikin. Karamar hukumar Faskari dai dake kudancin jihar Katsina bata da babbar asibiti inda babbar asibiti mafi kusa da su ita ce ta garin Funtua ko kuma ta garin Ƙanƙara. Haka zalika majalisar kuma ta amince a kashe sama da Naira miliyan 760 wajen gina cibiyar kula da masu ciwon koda a asibitin kwararru ta jihar wadda aka fi sani da asibitin kashi dake Batagarawa.

Gwamna Raɗɗa Ya Sauke Shugaban Hukumar Tattara Haraji Ta Jihar Katsina

Gwamna Raɗɗa ya sauke shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya cire sabon shugaban hukumar tattara haraji ta jihar. Wannan da na kunshe ne a cikin wata takardar da aka aikawa shugaban hukumar ranar Litinin, 19 ga watan Satumba, 2023 daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar. A cikin takardar, an bayyana cewa an cire shugaban hukumar ne biyo bayan janye tantancewar da majalisar dokokin jihar Katsina ta yi ma shi a kwanan baya. Mai karatu zai iya tuna cewa a kwanan baya ne Gwamnan ya tura sunan Prof Sani Mashi majalisar dokokin jihar Katsina domin su tantance shi a matsayin shugaban hukumar tattara haraji ta jihar. Bayan sun tantance shi, daga baya kuma sai majalisar ta ce ta gano wasu kurakurai a tattare da shi wanda kuma suka janye tantancewar da suka yi masa.

PTAD Sensitize Pensioners In Katsina On Newly Introduced “I Am Alive" Service

“I Am Alive" online confirmation of PTAD pensioners nationwide PTAD sensitize pensioners on newly introduced “I Am Alive" service The Pension Transitional Arrangement Directorate (PTAD) carried out a sensitization exercise of its ongoing “I AM AlIVE" online confirmation of pensioners under the Defined Benefits Scheme to retired workers in security sector, in an effort to identify pensioners that are alive for their prompt payment. The sensitization program took place on Monday, September 19, 2023, at the premises of the police compound at GRA in Katsina Metropolis. Speaking at the event, the leader of the exercise, Hajiya Bilkisu Rimi, said that the "I am Alive" program, which is being carried out, aims to determine the pensioners of the federal government who are alive by verifying themselves using the online program launched by the Directorate. Apart from that, she noted that the scheme was introduced looking at the current situation in the country to ease the untold hardship experienced by the retired workers in trying to get verified. She noted that the new introduced program would enable the pensioners to verify themselves using smart phone or computer laptop. According to her, in order to ensure prompt payment of pension to retired workers, it launched the scheme for the retired workers to verify themselves every six months. In his remark, Dr. Abubakar Dan Musa from the National Health Insurance Scheme (NHIS) said the cardinal objectives of the agency is to ensure the provision of health care delivery at subsidized rate. He noted that the NHIS would use the information gotten from PTAD to include retired workers in to the scheme, while calling on people to register with the agency to benefits with the agency. In another development, the leaders of the Directorate has paid a courtesy visit to the Emir of Katsina Dr. Abdulmuminu Kabir Usman and other traditional monarchs to continue to sensitize the pensioners on how to make good use of the opportunity introduced by PTAD. In a remark the Emir of Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, expressed his happiness over the introduction of the new scheme to ease the difficulty experience by the pensioners. The royal Father noted that the online confirmation of pensioners will ease the difficulties experienced by the retired workers for their payments. The Emir, added it will significantly impact on the lives of pensioners, who spent years contributing to the development of the nation. He called on them to live above board in discharging their assigned their responsibilities.

Majalisa Ta Buƙaci A Rufe Wurin Sharholiya Na Luna Otel Din-din-din Dake Garin Katsina

Majalisa ta buƙaci a rufe wurin sharholiya na Luna Otel din-din-din dake garin Katsina Majalisar dokokin jihar Katsina ta nemi Gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki matakin gaggawa na rufe shahararren otel din nan Luna dake a cikin garin Katsina. Ɗanmajalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Ali Abu Albaba shi ne ya gabatar da ƙudirin wanda ya samu goyon bayan illahirin ‘yanmajalisar dokokin. Kamar yadda Katsina Post ta rawaito, yayin gabatar da ƙudirin, ɗanmajalisar ya koka da gudummuwar da otel ɗin ke badawa wajen ɓata tarbiyar yara Mata musamman ƙananan Yara a Katsina. Hon. Albaba ya bayyana cewa Luna ta zama dandalin dake tara ‘yanmata ƙanana, da ake shan barasa da kuma mafaka ga miyagu masu aikata laifuka daban-daban. Haka kuma yace akwai sauran wuraren sharholiya dake a cikin garin Katsina waɗanda ya kamata Gwamnati ta rufe bisa ayyukan assha da akeyi da suka saɓa dokokin jihar. Yayi tuni ga zauren a kan dokar da ‘yanmajalisar suka yi na hana sha da sai da giya da wasu manyan laifuka a jihar wanda a cewar shi, Otel din Luna na ɗaya daga cikin wuraren da ake aiwatar da hakan. Hon. Albaba ya kara da cewa mafi yawancin masu buɗe wuraren ba ‘yan jiha ba ne kuma suna taimakawa wajen gurɓata tarbiyar ‘yan jihar Katsina. Ya roki zauren majalisar ya amince a tura ma ɓangaren zartarwa buƙatun majalisar domin a ɗauki matakin rufe otel din baki ɗaya.

Yadda Jerin Farashin Abinci Yake Yau Laraba A Wasu Kasuwannin Jihar Katsina.

Yadda jerin farashin Abinci yake yau Laraba a wasu Kasuwannin jihar Katsina. Kasuwar garin Ingawa,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 48,000 sabuwa - 39,000 2- Buhun Dawa - 35,000 Mori - 39,000 Fara - 34,000 3- Buhun Gero - 39,000 4- Buhun Maiwa - 38,000 5- Buhun Shinkafa - 76,000 shenshera - 25,000 6- Buhun Gyada - 59,500 Mai bawo - 25,000 7- Buhun Wake kana - 32,000 manya - 44,000 sabo - 31,000 8- Buhun Waken Suya - 33,000 9- Buhun Alabo - 38,000 10- Buhun Tarugu - 28,000 11- Buhun Dankali - 9,000 Kasuwar garin Danmusa, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 42,000 2- Buhun Dawa - 52,000 3- Buhun Gero - 37,000 4- Buhun Dauro - 49,000 4- Buhun Shinkafa - 68,000 Shanshera - 29,000 5- Buhun Gyada - 74,000 Mai bawo - 26,000 6- Buhun Waken suya - 38,000 7- Buhun Wake - 44,000 8- Buhun Aya - 43,000 kanana - 38,000 9- Buhun Alabo - 27,000 10- Buhun Tattasai - 23,000 11- Kwandon Tumatur - 5,600 12- Buhun Tarugu - 8,800 13- Buhun Dabino - 85,000 14- Buhun Barkono - 22,000 15- Buhun Dankali - 14,000 16- Buhun Albasa - 22,000 17- Buhun Tsamiya - 16,000 Kasuwar garin kankara, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 45,000 sabuwa - 32,000 2- Buhun Dawa - 42,000 3- Buhun Dauro - 42,000 4- Buhun Gyada - 75,000 5- Buhun Wake - 50,000 Sabo - 40,000 6- Buhun Waken suya - 32,000 7- Buhun Garin Kwaki - 28,000 8- Buhun Alabo - 42,000 9- Buhun Albasa - 20,000 10- Buhun Barkono - 20,000 Kasuwar garin Ajiwa a Karamar Hukumar Batagarawa, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - 37,000 2- Buhun Dawa - 45,000 3- Buhun Gero - 39,000 4- Buhun Gyada - 71,000 5- Buhun wake - 50,000 6- Buhun waken suya - 42,000 7- Buhun Alabo - 35,000 8- Buhun Albasa - 19,000 9- Buhun Dankali - 18,000 10- Buhun Barkono - 37,000 11- Buhun Garin Kwaki - 25,000 Kasuwar garin Bakori,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - sabuwa - 30,000 2- Buhun Dawa - 41,000 3- Buhun Gero - 54,000 sabo - 30,000 4- Buhun Dauro - 60,000 5- Buhun Alabo - 40,000 6- Buhun Gyada tsaba - 75,000 mai bawo - 23,000 7- Buhun Shinkafa tsaba - 70,000 shanshera - 28,000 8- Buhun Wake - 36,000 sabo - 46,000 9- Buhun waken suya - 38,000 10- Buhun Barkono - 37,000 11- Buhun Dankali - 16,000 12- Kwandon Tumatur - 2,000 kauda - 15,000 13- Buhun Tarugu - 21,000 14- Buhun Albasa - 26,000 lawashi - 1,800 Kasuwar garin Mashi,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - 44,000 sabuwa - 36,000 2- Buhun Dawa - 40,000 3- Buhun Gero - 34,000 4- Buhun Kalwa - 40,000 5- Buhun Sobo - 35,000 6- Buhun wake - 44,000 7- Buhun waken suya - 43,000 sabo - 36,000 8- Buhun tattasai - 40,000 9- Buhun Tumatur kauda - 19,000 10- Buhun Aya kanana - 38,000 manya - 47,000 11 Buhun Barkono - 18,500 12- Buhun Dankali - 15,000 13- Buhun Lalle - 13,000 Kasuwar garin funtua, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 52,000 sabuwa - 32,000 2- Buhun Dawa - 44,000 3- Buhun Gero - 34,000 4- Buhun Dauro - 5- Buhun Shinkafa - 76,000 samfarera - 25,000 6- Buhun Wake - 48,500 7- Buhun Waken Suya - 38,000 tsoho - 45,000 8- Buhun Tattasai - 9- Kwandon Tumatur- 2,500 10- Buhun Tarugu - 9,000 11- Buhun citta - 44,500 12- Buhun taki Yuri - 20,700 Daga Aysha Abubakar Danmusa.

Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta ƙirƙiro Wutar Lantarki A Wasu Asibitocin Jihar

Gwamnatin jihar Katsina za ta ƙirƙiro Wutar Lantarki a wasu asibitocin jihar Kwamishina lafiya na jihar Katsina yace a shirye-shiryen da Gwamna Raɗɗa yake don haɓɓaka kiwon lafiya a jihar, zai ƙirƙiro wutar lantarki domin bada wuta a wasu Asibitocin jihar Katsina nan da shekara mai zuwa. Kwashinan lafiya na jihar Katsina Dr. Bashir Gambo Saulawa shi ne ya bayyana haka a yayin kaddamar da kayayyakin gwaje-gwaje na cutar sida a Katsina wanda suka kaddamar tare da shugaban hukumar KATSACA Dr. Bala Nuhu Kankiya Sadaukin Kankia, a ranar Talata 19 ga watan Satumba 2023. Katsina Post ta samu cewa, daga cikin kayayyakin ayyuka a Asibitoci 347 dake faɗin jihar za a dauki wasu Asibitocin domin saka su cikin jerin waɗanda za a samar ma da wuta ta musamman don saka manyan kayan aikin da za a rinƙa gudanar da ayyukan kiwon lafiya ba sai an fita wata jiha ba. Kwashinan lafiyar yace Malam Dikko Umaru Raɗɗa yana nan a kan bakansa gameda samar da kayan ayyuka na zamani a ɓangaren kiwon lafiya a jihar Katsina, yace za su jajirce don ganin sun sauke nauyin da aka ba su a kowanne bangare a ma'aikatar kiwon lafiya.

Allah Ya Yi Ma Ɗanmasanin Kaita Rasuwa

Allah ya yi ma Ɗanmasanin Kaita rasuwa Ɗanmasanin Kaita, Malam Mustapha Dankama Allah ya yi ma sa rasuwa a Katsina Sheikh Mustapha Yusuf Dankama, wanda shi ne Ɗanmasanin Kaita Katsina Post ta samu rasuwar sa. An gudanar da jana'izarsa da misalin karfe 5:00 na yammacin Litinin 18 ga watan Satumba 2023 a gidansa dake Unguwar Taƙwiƙwi, Dankama a yankin ƙaramar hukumar Kaita dake jihar Katsina. Al'umma daban-daban ne sukai addu'a a gareshi a kan Allah ya yikansa da Rahama.