Ra'ayi: Da Ma Ni ɗan Takara Ne- Daga Yakubu Lawal

blog_post305.jpg

DA  MA NI DAN TAKARA NE.....

 'Daya daga cikin Adiban Marubutan Wakokin Turanci na Nijeriya a salon Pigin EZENWA OHAETO a wakarsa mai taken 'I wan bi President'ya yi irin wannan shaguben da na yi take da shi, wanda nasan hujjoji sune zasu tabbatar da hakan.
 
Duk da dai masanin mulki da kimiyyar siyasa Nicolas Macvelley yace ga dan siyasa da sandar hannunsa yake rama bugu, wato(Might is his right)salon da yan takara ke amfani da shi da sakon dake kunshe cikinsa bai isa ya sayarda dan takara ba,tare da jan ra'ayin masu zabe, ko dai don al'umma/masu zaben sun gaji da jin irin sakon ko kuma salon aika sakon ya zama tsohon yayi,musamman wannan lokaci da al'umma suka fi son kwai a baka fiye da kaza a akurki.

Duk da cewar,a kakar zabe ta bana masu takara daga Jam'iyu dabam-daban sun yi kokarin gane cewar zamani ya fara canzawa sun gane ba a cika bin Yarima a sha kida ba,abin nufi kowane dan takara yanzu ya na lika hotonsa da  tambarin Jam'iyarsa ne kawai, sabanin abaya da wasu ke hada hotonansu da wasu da suke ganin za su zamar masu  albarkacin kaza,kadangare ya sha ruwan kasko,amman sakon iri daya ne da na baya, kodai na yi alkawarin zan yi...
ko kuma zan yi abinda wane ya kasa yi da dai sauransu.

DA MA NI DAN TAKARA NE! To da  sai in yi la'akari da abinda na ke jin al'umma/masu zabe na koke da shi game da salon  mulkin da ake ciki,in yi kwaskwarima in fiddowa al'umma,tare da yin amfani da shi a duk lokacin da na hau bisa munbarin yakin neman zabe,don kaucewa maimaita abinda a kan kushe.
Alal misali mafi akasarin abinda masu zabe suke koke da zargin mahukunta sune tarayya da'yan hana ruwa gudu,rashin hukunta masu laifi,rashin daukar mataki kan matsaloli a zahiri,rashin bin kadi a kan wadanda suka daurawa aikin al'umma da sanyawa kowa ido ya yi abinda ya yi masa dadi da makamantansu, duk da dai zargi ne irin na mai mulki da wanda ake mulka, domin suma masu mulkin suna cewa sunyi abin a yaba da yakamata.

Kodayake,akwai yiwuwar salon siyasar ne ya nuna, yin alkawarin dorawa daga inda wanda ya rikewa dan takara kan macijin yake wasa da bindin, to amman DA MA NI DAN TAKARA NE,to ba zan yi alkawari ba tunda wuyar cikawa gareshi,sai in cewa al'umma su zabe ni tare da ta ya ni addu'ar samun nasara cikin sauki da sauke nauyin mulkin cikin sauki,in anyi nasara,tunda a fili take, ba tarurun taron yakin zabe ke haifar da mafi rinjayen nasara a zabe ba,don kila duk sojojin baka ne da ake wa kirarin sun fi mai katin kada kuri'a.

To amman wani hanzari ba gudu ba,zan so al'umma su goya mani baya, don ka da su yi ta zundena tare da hadani da wanda ya yi mani hanyar zama dan takarar, ya kama ni da laifin rashin yin alkawari irin nasa na cewa zan dora daga inda ya tsaya,domin akwai yiwuwar daga inda shi (mai gidan nawa)ya tsaya, watakila ba nan al'umma ke bukatar a fara mulkarsu ba.

DA MA NI DAN TAKARA NE! Zan yi kokarin al'umma su fahimci manufata kafin manufar iyayen gidana,zan tabbatar na gamsar da wadanda nike tunanin zasu zabe ni,ba ki dayansu ba wadanda na tara a wurin gangamin yakin neman zabe ba kadai,saboda ba kowane mai halartar yakin neman zaben ba ke iya zabe na,sannan zan yi kokarin fahimtar matsalar da wanda nike son in gada ya fuskanta  ko da kuwa ba Jam'iyarmu daya ba, don kauce ma ta, daga nan sai in barwa Allah sauran tun da shi ke bayarda mulki ga wanda ya so, a kuma sanda ya so.

Kash!!! Da ma ace shugannin da ke da magada daga cikin Jam'iyunsu za su yi jarunta irinta Gwamnan Jahar Kaduna a lokacin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar Gwamna na Jam'iyarsa?" A inda Gwamnan yace ina kaddamar maku da Malam Uba Sani a matsayin dan takarar Gwamna,ku zabe shi mutanen kirki ne, harma ya fini kirki,kuma karku tuhumeshi a kan kuskuren da na aikata a yayin tafiyar da mulkina. Sai dai ina neman ku yafe mani nima a kan kurakuren da na yi."Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan  labari.

Irin wannan salon aika sako,salo da ka iya canza tunanin makiyi ya koma masoyi,kuma sabon salo ne a siyasar Nijeriya.

To tunda yanzu NI BA NI CIKIN  'YAN TAKARA sai mu taru mu fahimci, miye hakkinmu,miye hakkin wadanda zamu zaba,in har matsalolin da muke zargi ba laifinmu bane, don gujewa gudun da babu mafita, wanda karshensa safkon bubukuwa.

Alkalamin Yakubu Lawal 
Dan Jarida
Jami'in Hulda da Jama'a


Comment As:

Comment (0)