Jihar Katsina A Hannun Malan Dikko Radda: Dama Da Kuma Kalubalen Da Ke Gaban Ta
- Posted By: Mustapha Saddiq --
- Thursday, 01 Jun, 2023
- Reporter : Mallam Mustapha
Katsina State A Karkashin Malan Dikko Radda: Dama da kuma Kalubalen da ke gaban ta - Daga Hon. Abdullahi Ibrahim Mahuta
Tun bayan dawowar mulkin damokiradiyya a kasar nan a cikin shekarar 1999, jahar katsina ba ta taba samun wata irin dama ta musamman ba, kamar wadda ta samu yanzu a karkashin shugabancin gwamnati mai ci yanzu ba.
Da farko dai, gwamnatin Dr. Dikko Radda, ita ce gwamnati ta farko a jihar Katsina, tun daga 1999, da ta hau gadon mulki ba tare da tallafawar wasu jigajigan yan siyasa ba, wadanda ake gani, su ma kuma su ke ganin kan su, cewa ba wata gwamnati da ta isa ta hau gadon mulki ba tare da taimakon su ba. Wannan dalilin ne ma ya sa shi da kan shi mai girma gwamna, a wurare daban-daban, ya kan bugi kirji tare da alfaharin cewa shi ba yaron kowa ba ne.
Wannan dama, ta sa wannan gwamnati ta hau mulki ba tare da nauyin bashin wasu manyan ma su kudi ba, wadanda akan yi ma zargin cewa su ke takura gwamnati, su hana ta gudanar da ayyukan cigaban jiha da talakawa baki daya. Su kan yi hakan ne kuma ta hanyar cusa yaran su cikin gwamnati, ba domin chanchantar su ba, sai domin kare muradun su a maimakon muradun talakawa baki daya.
A bisa wannan dalili kenan, duk mutumin da aka gani a cikin wannan gwamnati, to mutun ne wanda ita gwamnatin ta kawo shi da kan ta, domin ta aminta da ingancin shi da kuma sahihancin shi. Ba wai mutun ne wanda wani babba ya cusa ma ta ba.
Dama ta biyu kuma da wannan gwamnati ta samu, ita ce ta kasancewa gwamnati ta farko da yan takarar gwamna guda uku da su ka fafata wajen zaben fidda gwani, su ka zama gwamna, mataimakin gwamna da kuma sakataren gwamnati. Wannan dama ce mai kyau. Domin idan su ukkun su ka hada manufofin da su ke da su domin ci gaban jihar a wuri guda, to lallai akwai kyakkyawan zaton cewa jihar katsina za ta samu alkhairai ma su yawa, in shaa Allah.
Hakanan kuma ta bangaren ilimi da gogewar aiki, jihar Katsina ba ta taba samun wani team ba na gwamna, mataimakin gwamna da kuma sakataren gwamnati, wanda su ka hada ilimi da gogewar aiki, musamman a mataki na tarayya ba kamar wanda mu ke da shi yanzu. Dukkan su makusanta ne na kusa da gwamnatin da ta sauka. Biyu daga cikin su kuma sun kwashe shekaru a gwamnatin tarayya. Saboda haka, rashin sanin makamar aiki, ko rashin sanin abinda gwamnati ke ciki, bai ma taso ba.
A bisa wadannan dalilai ne, jama'a ke ganin gwamnati mai ci yanzu fa ba ta da wani uzuri da zai hana ta cika alkawurran da ta daukar ma talakawa domin Allah ya ba ta dukkan wata dama da ta ke bukata, musamman damar cin gashin kan ta ba tare da sa bakin wasu manya manyan attajiran siyasa ba.
Sai dai babban kalubalen da ke gaban ta shine na dinbin bashin da ta gada daga gwamnatin da ta wuce. Wannan bashi kuwa, idan aka fara cire shi daga source, to ba karamin kalubale gwamnati da mutanen Katsina za su fuskanta ba. Domin hakan zai kawo babban tarnaki a kokarin gwamnatin na samar da romon damokiradiyya ga talakawa. Wannan ya sa akwai bukatar gwamnati ta yi hanzarin nemo wasu sababbin hanyoyin samun kudin shiga domin magance waccan kalubale da ta ke fuskanta.
Wani kalubalen kuma da gwamnati mai ci yanzu za ta fuskanta shine na yawan alkawurran da ta ke yi wadanda ke kara daga tsammani, da kwadayin talakawa a kan romon damokiradiyya. Wanda idan hakan bai samu ba kuma, zai janyo hushin talakawa da raina kokarin ita gwamnatin akan abubuwan da ta samu halin yi. Expectations bring disappointments.
Allah ya yi ma na jagora