Dr. Dikko Raɗɗa: Zuwa Da Kai Yafi Saƙo - Maiwada Ɗammalam

blog_post985.jpg

DR. DIKKO UMAR RADDA: ZUWA DA KAI YAFI SAK’O — Maiwada Dammallam 

Dr. Dikko Radda yayi jawabi mai sosa rai a cikin jawaban shi a Faskari da Sabuwa. Ya fadi cewa matsalar rashin tsaro matsala ce da shafi kowa kuma ba magana ce da za’a siyasantar ba kamar yadda wasu ke yi. Ya kara da cewa ba gaskiya bane ace masu mulki basu san inda matsalar ta kai ba. Ya bada misali da kanshi, yace matsalar rashin tsaro ta shafe shi kai tsaye kuma ya jita a jikin shi kamar yadda mutunen yankin suka jita. Yace yan ta’adda sun kashe wanshi sun kuma yi garkuwa da wani wan nashi har sai da aka biya kudin fansa. Kenan shi ba jita-jita yaji ba maganar rashin tsaro, ji a jikin shi yayi. Hakan kuma yasa yana da masaniyar irin k’unci da rad’ad’in rashin tsaro da mutanen Jihar Katsina suke ciki; ya kuma sa mashi zimmar yin duk abinda yakamata don kawo karshen matsalar. 

Wannan jawabi yasa na kara fahimtar dalilin da yasa ya fidda tsoro, yake shiga lungunan da ake tunanin basu shiguwa saboda rashin tsaro don ya iske mutanen, ya jajanta masu, ya kuma tabbatar masu da damuwar shi kan matsalar da kuma niyyar shi ta sama ma Jihar Katsina zaman lafiya da walwala. Kamar yadda Hausawa ke cewa, “Mai kamar zuwa ake aike.” Duk wanda yayi tunanin irin halin da wanda yan ta’adda suka kashe ma wa, suka kuma sace wani wan ya shiga, to zai fahimci Dr. Radda baya daga cikin wadanda zasu siyasantar da maganar rashin tsaro ko suyi mata rikon sakainar kashi. 

Kamar yadda kuma Hausawa ke cewa inda yaro ya tsinci kwabo nan yafi saurin tunawa, to ba inda ya tsinci kwabo kawai yafi saurin tunawa ba, har da inda ya yada kwabo. Kenan, maganar rashin tsaro a Jihar Katsina rubuce take a zuciyar Dr. Radda. Idan aka jingina haka da jajircewar shi na shiga ko wane lungu don ya gabatar da kanshi ya kuma baje kolin kudurorin gwamnatin da zai jagoranta take niyyar aiwatar wa, to zai yarda cewa maganar ga wuta ga masara ce — mai kamar zuwa ne za’a aika. 

Zuwa yanzu dai kam Dr. Radda ya ciri tuta cikin yan takarar Gwamna, bama a Jihar Katsina ba kawai, a Najeriya baki daya. Da wahala ka samu dan takarar da ya zageye Jihar shi gaba daya; ya shiga kowane lungu da sak’o kamar yadda Dr. Radda yayi, kuma yake cikin yi ba. Idan kuma an samu, ban tsanmanin akwai wanda yake a Jihar dake da hatsarin yin hakan kamar Jihar Katsina ba. Hakika, wannan yana nuni da irin jajirtaccen Shugaban da za’a samu ne idan har Allah tabbatar da jagoranci Jihar Katsina a hannu Dr. Radda. 

Dr. Radda ba’a manyan biranen Kananan Hukumomi yake tsayawa a kira mashi Dagatai da Masu Unguwanni da talakawan su ya gana da su ba. Kauyukan su da rugagen su yake iske su, ya girmama su, yaga matsalolin su da idon shi sannan ya nemi alfarmar su don a hada hannu a saita lamuran Jihar Katsina. Ko ba komai ya daga farashin siyasa da kuma martabar talaka mai jefa kuri’a a Katsina. Yanzu dai ba dan kasuwar siyasar da zaiyi zaune birne yana kira wakilai, yana basu kudi sukai labarin shi kauye suna kwantancen shi da fosta lik’e jikin icce. To a kula, wanda yazo yafi wanda bai zo ba kama da zai dawo. 

Allah Ya zaba ma Katsina abinda yafi alkhairi.


Comment As:

Comment (0)