Labarai

Za'a Kashe Naira Biliyan 26.6 Wajen Magance Ambaliyar Ruwa A Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ware Naira biliyan 26.6 wajen magance ambaliyar ruwa da zaizayar Ƙasa a jihar Katsina. Ya bada tabbacin matakan da gwamnatin ta ɗauka na magance ambaliyar ruwa da zaizayar Ƙasa a jihar. Hon. Musa Adamu ya jinjina ma Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa da irin kokarin da take na inganta rayuwar al'ummar jihar baki ɗaya. Katsina Post ta samu cewa hukumar NIMET ta lissafa jihar Katsina a cikin jerin jihohin da zasu fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a Najeriya. Matakan da gwamnatin ta ɗauka kamar yanda Kwamishinan ya ambata sun haɗa da samar da shirin kare muhalli guda 13, wayar da kan al'umma akan shirin inganta muhalli, kwashe shara dake kan magudanan ruwa, da kuma ginawa da faɗaɗa magudanan ruwa a jibia. Kwamishinan yayin da yake tabbatar da ƙudurin gwamnatin Gwamna Dikko Radda na ci gaba da bunƙasa a jihar, ya ce jihar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace da suka haɗa da inganta daji, dashen itatuwa, da kawar da ramuka da sauran su a cikin kwanaki 100 na farko da Gwamnan jihar yayi a ofis.

Allah Ya Yi Ma Yayan Hajiya Turai Umar Musa Yar'adua Rasuwa

Allah ya yi ma Yayan Hajiya Turai Umar Musa Yar'adua rasuwa Kamar yadda Katsina Post ta samu daga Focus News, tsohan shugaban hukumar kula da ma'aikatan jihar ya rasu. Tsohan shugaban hukumar kula a ma'aikatan jihar Katsina wanda shi ne ya kasance yaya ga uwargidan tsohan shugaban ƙasar Najeriya, Hajia Turai Yar'adua, Alhaji Zayyana Abdullahi Mai Maje, ya rasu daren jiya Talata a wata Asibiti dake garin Kano. An gudanar da jana'izarsa a ranar Laraba 13 ga watan Satumba 2023 da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidansa dake Unwala kusa da gidan Alhaji Bilya Sanda a cikin birnin Katsina. Malamai da dama ne sukai addu'a a gare shi a kan Allah ya jiƙansa da Rahama.

Gwamna Raɗɗa Ya Sassauta Dokar Hana Hawa Babura Zuwa Ƙarfe 10 Na Dare

Gwamna Raɗɗa Ya Sassauta Dokar Hana Hawa Babura Zuwa Ƙarfe 10 Na Dare Gwamnatin Jihar Katsina ta sassauta dokar takaita zirga-zirgar babura da 'yan kurkura daga karfe goma na dare zuwa shidda na safe maimakon karfe takwas na dare zuwa karfe shidda na safe. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa data fito daga ofishin kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida ta fitar a jiya Talata, wacce Tukur Hassan Dan-Ali ya sa ma hannu. Hakan ya biyo bayan taron majalisar tsaro da ya gudana a ranar Talata 12 ga Satumba a shekarar 2023 a gidan gwamnatin jihar. Bayan gudanar da taron, a yanzu dokar hana zirga-zirgar Babura da Ƙurƙurori za ta fara aiki ne daga karfe goma na dare zuwa shida na safe a kullum maimakon karfe takwas na yamma zuwa shida na safe da aka saba tun da farko. Kwamitin Tsaron ya kuma gode wa dukkan mutanen da ke zaune a wadannan kananan Hukumomin bisa hadin kai da goyon bayan da ake ba Gwamnati da Hukumomin tsaro game da wannan doka. Sanarwar ta cigaba da cewa, Gwamnati na aiwatar da tsare-tsare da kokarin kawo karshen kalubalen tsaro a jihar. Idan dai za a iya tunawa kananan Hukumomin da wannan doka ta hana zirga-zirgar Babura da Yan ƙurƙurori ya shafa sune, Jibia, Batsari. Safana, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa, Dandume, Danja, Funtua, Ƙafur, Malumfashi, Musawa, Matazu, Bakori, Dutsinma, Kurfi, Kankia da Charanchi.

Gwamna Raɗɗa Ya Rattaba Hannu Kan Ƙarin Kasafin Kuɗi Na Biliyan 300

Gwamna Raɗɗa Ya Rattaba Hannu Kan Ƙarin Kasafin Kuɗin Biliyan 300 Gwamnan Katsina Dikko Radda ya rattaba hannu kan karin kasafin kudi sama da biliyan 300.6 na shekarar 2023 Daukar matakin ya nuna aniyar gwamnati na ba da fifiko ga jin dadin 'yan jiha da samar da yanayi mai aminci da wadata ga dukkan mazauna jihar Karin kasafin kudin shi ne domin yaki da rashin tsaro, rage radadin talauci, da bayar da tallafi ga marasa galihu a fadin jihar Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya rattaba hannu kan karin kasafin kudi sama da biliyan 300.6 na shekarar 2023. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed,shi ne wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi. Ya ce za a tura karin kasafin kudin ne domin yaki da rashin tsaro, rage radadin talauci, da bayar da tallafi ga marasa galihu a fadin jihar. Ya ce kakakin majalisar dokokin jihar, Nasir Yahya-Daura ne ya mika wa gwamnan karin kasafin kudin a ranar Juma’ar da ta gabata. "Wannan matakin ya nuna aniyar gwamnati na ba da fifiko ga jin dadin 'yan jiharta da samar da yanayi mai aminci da wadata ga dukkan mazauna jihar," in ji Mohammed. Da yake jawabi a wurin rattaba hannun, Radda ya bayyana fatan cewa karin kasafin zai taimaka wajen ciyar da jihar gaba da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga mazauna yankin. Ya yabawa ‘yan majalisar bisa namijin kokarin da suka yi wajen tsara kasafin, ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa. Hakazalika gwamnan, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin kasaftawa da amfani da albarkatun kasa domin ci gaban jihar. Majiyar Jaridar Katsina Post ta DAILY POST ta rahoto cewa Radda ya bukaci majalisar ta amince da karin kasafin kudin domin kara kasafin kudin shekarar 2023 na Naira biliyan 289.6 wanda tsohon gwamnan jihar Aminu Masari ya sanya wa hannu a watan Disambar shekarar 2022.

MSF Na Karɓar Yara 5,000 Masu Ciwon Yunwa Duk Wata A Katsina

MSF na karɓar Yara 5,000 Masu Ciwon Yunwa duk wata a Katsina Dangane da matsalar ƙarancin Abinci mai gina jiki a jihar Katsina, ƙididdigar da ƙungiyar MSF ta yi ta gano cewar duk wata tana karɓar Yara sama da 5,000 a Katsina Kamar yadda Katsina Post ta samu daga Vanguard, shugaban ƙungiyar ayyuka ta ƙungiyar Mallam Hassan Issa, shi ne ya bayyana cewar ko a lokutan baya sun shaida cewar suna karbar yara kwatankwacin hakan. Inda ƙungiyar MSF ta bayyana cewa matsalar ƙarancin Abinci mai gina jiki a jihar Katsina ya kai ƙololuwa, inda kungiyar likitoci ta MSF ta ce an samu ƙaruwar masu ɗauke da cututtukan yunwa daban-daban inda adadin yawan su ya zarce 400 a kowace rana, wanda hakan ya kai ga ƙiyasin sama da 5,000 ne ke ziyarartar MSF a kowanne Wata. A cewar sa a sati ɗaya aƙalla Yara 600 zuwa 700 a suke karɓa a cibiyoyinsu, amma tsakanin watan Agusta da Satumba, rashin abinci mai gina jiki, sun shirya don ganin yadda Yara sama da 10,000 ake karɓarsu a kowane Wata.

Yanzu-Yanzu: An Fidda Sakamakon Jarabawar Daukar Malaman Makaranta A Katsina

Yanzu-Yanzu: An fidda sakamakon jarabawar daukar malaman makaranta a Katsina Kwamitin da Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya kafa domin tantancewa tare da gudanar da jarabawar ɗaukar Malaman makarantun Firamare da Sakandire ya fitar da sakamakon jarabawar. Shugaban kwamitin, Dr. Sabiru Ɗahiru ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a hedikwatar ma'aikatar ilimin bai-ɗaya ta jihar Katsina. A cewar sa, cikin malamai sama da 7,600 da suka zauna jarabawar, malamai 7,325 sun yi nasara kuma Gwamna Raɗɗa ya amince a ɗauke su aiki na din din din nan take. Dr. Sabiru ya kara da cewa Gwamnan kuma ya bayar da umurnin horar da duka Malaman da za'a dauka nan take kafin daga bisani a tura su zuwa makarantun da za su fara koyawa.

'Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kurfi Zuwa Dutsinma

Matafiya sun shiga halin fargaba a yayin da yan bindiga suka tare hanyar Kurfi zuwa Dutsinma. Wani wanda ya shaida afkuwar lamarin ya ce yan bindiga sun shiga garin Birchi a ƙaramar hukumar Kurfi da misalin ƙarfe 4:30pm na rana dauke da makamai. Ya bayyana cewa 'yan bindigan sun kwashi dabbobi a garin amman babu tabbacin ko sun dauki mutane. Yace harin yayi sanadiyar tilasta ma al'ummar garin shiga fargaba da matafiya dake bin hanyar. Sai dai yace tuni 'yan sanda suka bi sawun 'yan bindigar sakamakon bayanai da suka samu.

Maidabino Investment