Labarai

Sa'in Katsina Ya Cika Shekaru 50 Cif A Sarautarsa

Sa'in Katsina Ya Cika Shekaru 50 Cif A Sarautarsa Maigirma Sa'in Katsina Amadu na Funtua ya cika shekaru 50 cif a sarautar Sa'in Katsina. Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa a ranar 16 ga watan Satumba a shekarar 1973 ne aka naɗa Alhaji Amadu Na Funtua a matsayin Sa'in Katsina, inda jiya 16 ga watan Satumba 2023 ya cika shekaru 50 cif a bisa Sarautar Sa'in Katsina. Kamar yadda Katsina Post ta samu, Marigayi Sarkin Katsina Alhaji Dr. Usman Nagogo, shi ne wanda ya naɗa Alhaji Amadu na Funtua a shekarar 1973 a matsayin Sa'in Katsina. Sa'in Katsina Amadu na Funtua, a yanzu yana da shekaru 94 a duniya wanda yana daga chikin mutanen da suka yi tsawon rai cikin waɗanda aka baiwa sarauta a tun a wancen lokacin. Al'umma da yawa ne sukai Addu'ar a gareshi a kan Allah ya ƙara ma shi lafiya da nisan ƙwana.

An Kama Wani Kasurgumin Dan Bindiga A Katsina

An kama wani kasurgumin dan bindiga a Katsina Rundunar Ƴan Sandan jihar Katsina ta kama wani ƙasurgumin ɗan ta'adda mai suna Saminu Usman ɗan asalin ƙaramar hukumar Jibia, wanda ake zargi da yin garkuwa da mutane. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar a madadin Kwamishinan ƴan sandan jihar. A cewar ASP Abubakar rundunar a ƙoƙarin ta na yaƙi da ƴan ta'adda da ta'addanci a jihar Katsina, ta samu nasarar cafke wani Saminu Usman mai shekaru 19 ɗan asalin ƙaramar Jibiya da ake zargi da aikata laifin yin garkuwa a ƙauyen tashar Hurera da ke cikin jibiya. ASP Abubakar Sadiq ya ƙara da cewa a ranar da akayi garkuwar, an kawo rahoton sace ɗan shekara 5 mai suna Usman Shu'aibu a ofishin ƴan sanda na Jibiya ta hanyar wani Shu'aibu Salisu ɗan asalin garin. A cewar sa, bayan ya tuntuɓi mahaifin yaron, ya buƙaci a biya shi Naira dubu 600,000.00 da wayar Android guda uku a matsayin kuɗin fansa, wanda uban ya biya ya amso ɗan sa. ASP Abubakar, ya bayyana cewa, bayan samun rahoton, jami'an rundunar suka bazama neman wanda ya aikata ta'addancin tare da gano shi a garin Lambata na jihar Naija. Kakakin rundunar yace a lokacin binciken, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin tare da fadin cewar ya haɗa kai wajen ɗauke wani Rabe.

Jerin Yadda Farashin Abinci Yake Jiya Juma'a A Wasu Kasuwannin Jihar Katsina

Jerin yadda farashin Abinci yake Jiya Juma'a a wasu Kasuwannin jihar Katsina Kasuwar garin Dandume, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara fara - 54,000 ja -56,000 ja sabuwa- 36,000 sabuwa - 34,000 2- Buhun Dawa - 52,000 3- Buhun Gero - 36,000 4- Buhun Dauro - 56,000 5- Buhun Rogo - 32,000 6- Buhun Dabino - 90,000 7- Buhun Wake - 55,000 ja - 65,000 8- Buhun waken suya - 37,000 9- Buhun Aya - 52,000 kanana - 42,000 10- Buhun Gyada tsaba- 82,000 mai bawo - 21,000 11- Buhun Shinkafa tsaba - 86,000 shenshera - 36,000 ta tuwo - 80,000 12- Buhun Dankali - 18,000 13- Buhun Alkama - 51,000 14- Buhun Kalwa - 43,000 wankakka 55,000 15- Buhun Tattasai - 10,000 kauda - 40,000 16- Kwandon Tumatur - 5,000 kauda - 20,000 17- Buhun Tarugu - 15,000 solo - 7,000 18- Buhun Albasa - 20,000 19- Buhun Barkono - 35,000 Kasuwar garin Bindawa,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - 48,000 Sabuwa - 36,000 2- Buhun Dawa ja - 40,000 fara - 36,000 3- Buhun Gero - 30,000 4- Buhun Alabo - 28,000 5- Buhun Gyada tsaba - 65,000 mai bawo - 30,000 6- Buhun Shinkafa tsaba - 70,000 shanshera - 28,000 7- Buhun Wake kanana - 44,000 8- Buhun waken suya - 40,000 9- Buhun Tafarnuwa - 35,000 10- Buhun Dankali - 22,000 11- Buhun Tattasai Danye - 8,000 kauda- 47,000 12- Kwandon Tumatur - 2,500 13- Buhun Tarugu - solo - 14,000 14- Buhun Albasa - 25,000 15- Buhun Gishiri - 10,000 16- Buhun Citta - 35,000 17- Buhun Kanwa - 9,000 18- Buhun Barkono - 20,000 Kasuwar garin Dutsanma ,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Tiyar masara tsohuwa - 1,50 2- Tiyar Dawa - 900 3- Tiyar Gero - 800 sabo - 800 4- Tiyar Shinkafa - 2,100 5- Tiyar Gyada tsaba - 1,300 samfarera - 450 tsohuwa - 650 6- Tiyar waken suya - 1,100 7- Tiyar wake - 1,300 sabo - 1,300 8- Tiyar Alkama - 1,200 9- Tiyar Ridi - 2,100 10- Buhun Tattasai - 18,000 11- Buhun Tarugu Danye - 20,000 12- Kwandon Tumatur - 5,000 13- Damin Albasa - 1,000 14 Tiyar Barkono - 1,000 15- Buhun Dankali - 15,000 Makani - 18,000 Kasuwar garin Kankiya,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 36,000 2- Buhun Dawa - 40,000 3- Buhun Gero - 30,000 4- Buhun Gyada - 68,000 mai bawo - 22,000 5- Buhun Wake - 44,000 6- Buhun waken Suya - 40,000 7- Buhun Alkama - 56,000 8- Buhun Tattasai - 17,000 9- Kwandon Tumatur - 2,500 10- Buhun Tarugu - 15,000 11- Buhun Albasa - 20,000 Kasuwar garin Daura, ga yadda fara shin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 50,000 Sabuwa - 37,000 2- Buhun Gero sabo - 34,000 3- Buhun Dawa - 56,000 4- Buhun Alkama - 46,000 5- Buhun Gyada - 70,000 6- Shinkafa Tsaba - 75,000 _ 80,000 7- Buhun Wake fari Sabo - 39,000 ja sabo - 38,000 8- Buhun Waken Suya - 42,000 9- Kwandon Tumatur - 12,000 10- Buhun Tattasai solo - 12,000 11-Buhun Tarugu - 20,000 kore 20,000 12- Buhun Albasa - 25,000 Daga Aysha Abubakar Danmusa

Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Da Ya Bi Ta Katsina Zuwa Maradi A Shekarar 2025

Za a kammala aikin titin Jirgin Ƙasan da ya bi ta Katsina zuwa Maradi a shekarar 2025 Ana ci gaba da shirye-shiryen kammala Aikin Titin jirgin kasan da ya taho daga Dawanau a jihar Kano zuwa Daura har cikin Katsina zuwa Maradi. Ministan sufurin, Alhaji Sa'idu Alƙali ya yi jawabin hakan ne a ranar Jumma'a, lokacin da ya jagoranci ziyarar duba aiki a ma'aikatar. A cewar sa duk abinda suka zo dubawa sun gani kuma bada jimawa ba za a kammala ayyukan cikin sauki da lumana ba tare da tsangwama ba tare da kuma ƙyayyade ayyukan 'yankwangilar. Kamar yadda Katsina Post ta samu, Ministan ya yi bayanin cewa an yi babban aiki wanda idan aka kammala shi zai dade ana amfanarsa bai lalace ba domin ayyukan akwai manufofi ma su kyau. Yace babbar kwangilar wadda take a ƙarƙashin jagoranci, Mr. Vadislav Bystreneko, ya ce yarjejeniyar da sukai da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2021 ta kasance kimanin kuɗi dala biliyan 1.95 kuma sun sanya hannu kan ayyukan tare da alƙawarin kammalawa. Alhaji Sa'idu Alkali, ya ƙara da cewa tunda kafin a sake kudin ayyukan, sun ci gaba da wasu manyan ayyuka na zane-zanen, da binciken ƙasa, da kuma kulawa da ayyukan kwangilar. Daga ƙarshe Mr. Vladislav Byststeko yace gwamnatin tarayya ta kwantar da hankalinta gameda kammala aikin domin sun yanke shawara za su kammala ayyukan a shekarar 2025 domin aikin yana da matuƙar muhimmanci a yankunan Arewa. Idan baku manta ba, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shi ne ya bada aikin titin jirgin ƙasan tin lokacin shugabancin sa na shugaban kasar Najeriya.

Za'a Fara Tantance Daliban Da Za'a Ba Tallafin Karatu A Katsina⁩

Hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Katsina ta ce za ta fara bayar da tallafin karatu ga dalibai yan asalin jihar Katsina da suka samu guraben a duk manyan makarantun jihar a ranar 18 ga watan Satumba. Kakakin hukumar Salisu Lawal Kerau ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Katsina. Ya ce za a kammala biyan tallafin ne a ranar 9 ga watan Oktoba a manyan makarantu daban-daban na Katsina da kewaye. Don haka ana buƙatar duk sabbin ɗalibai su zo tare da kwafin takardar rajista, ko remitta, da ingantaccen katin shaida na makaranta, kafin karɓar shedar samun tallafin. Ya bayyana cewa da zarar an fara raba kudaden tallafin, za a fara ba tallafin ga ɗalibai yan asalin jihar Katsina dake a manyan makarantun jihar. Ya tabbatar da cewa daga baya hukumar za ta cigaba da bada tallafin ga sauran dalibai yan asalin jihar da ke karatu a dukkanin manyan makarantun ƙasar nan.

Allah Ya Yi Ma Maigarin Wurma Dake Yankin Kurfi Rasuwa

Allah ya yi ma Maigarin Wurma dake yankin Kurfi rasuwa Alhaji Mustapha Muhammad Ɗandaɗi dake yankin kurfi a jihar Katsina ya rasu. Maigarin Wurma dake ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Ɗandaɗi Allah ya karɓi rayuwarsa a daren jiya Laraba 13 ga watan Satumba 2023. An gudanar da jana'izarsa da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Alhamis 14 ga watan Satumba 2023 a gidansa dake Unguwar Ƙadangaru dake ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina. Al'umma da dama ne suka yi addu'ar Allah ya jikansa da Rahama.

Yadda Jerin Farashin Abinci Yake Jiya Laraba A Wasu Kasuwannin Jihar Katsina

Yadda jerin farashin Abinci yake Jiya Laraba a wasu Kasuwannin jihar Katsina Kasuwar garin Ingawa,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 48,000 sabuwa - 39,000 2- Buhun Dawa - 35,000 Mori - 38,000 Fara - 34,000 3- Buhun Gero - 38,000 sabo - 30,000 4- Buhun Dauro - 38,000 5- Buhun Shinkafa - 79,000 shenshera - 26,000 6- Buhun Gyada - 60,000 Mai bawo - 26,000 7- Buhun Wake - 48,000 sabo - 40,000 8- Buhun Waken Suya - 39,000 9- Buhun Alabo - 32,000 10- Buhun Tarugu - 28,000 11- Buhun Dankali - 9,000 Kasuwar garin Danmusa, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 56,000 sabuwa - 42,000 2- Buhun Dawa - 43,000 3- Buhun Gero - 30,000 4- Buhun Dauro - 49,000 4- Buhun Shinkafa - 68,000 Shanshera - 29,000 5- Buhun Gyada - 74,000 Mai bawo - 26,000 6- Buhun Waken suya - 38,000 7- Buhun Wake - 52,000 8- Buhun Aya - 41,000 kanana - 38,000 9- Buhun Alabo - 27,000 10- Buhun Tattasai - 22,000 11- Kwandon Tumatur - 5,600 12- Buhun Tarugu - 8,800 13- Buhun Dabino - 85,000 14- Buhun Barkono - 22,000 15- Buhun Dankali - 14,000 16- Buhun Albasa - 21,000 17- Buhun Tsamiya - 16,000 Kasuwar garin Mararrabar kankara a karamar hukumar Malumfashi, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 47,000 sabuwa - 34,000 2- Buhun Dawa - 42,000 3- Buhun Dauro - 55,000 _ 54,000 4- Buhun Gyada - 73,000 5- Buhun Wake - 55,000 6- Buhun Waken suya - 37,000 7- Buhun Garin Kwaki - 23,000 8- Buhun Alabo - 46,000 9- Buhun Albasa - 20,000 Kasuwar garin Ajiwa a Karamar Hukumar Batagarawa, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - 50,000 sabuwa - 40,000 2- Buhun Dawa - 50,000 3- Buhun Gero - 38,000 4- Buhun Gyada - 71,000 5- Buhun wake - 50,000 6- Buhun waken suya - 40,000 7- Buhun Alabo - 38,000 8- Buhun Albasa - 20,000 9- Buhun Dankali - 18,000 10- Buhun Barkono - 35,000 11- Buhun Garin Kwaki - 26,000 Kasuwar garin Bakori,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - 50,000 sabuwa - 29,000 2- Buhun Dawa - 45,000 3- Buhun Gero - 54,000 sabo - 35,000 4- Buhun Dauro - 60,000 5- Buhun Alabo - 50,000 6- Buhun Gyada tsaba - 72,000 mai bawo - 23,000 7- Buhun Shinkafa tsaba - 85,000 shanshera - 28,000 8- Buhun Wake - 60,000 sabo - 46,000 9- Buhun waken suya - 38,000 10- Buhun Barkono - 35,000 11- Buhun Dankali - 16,000 12- Kwandon Tumatur - 1,300 kauda - 19,000 13- Buhun Tarugu - 20,000 14- Buhun Albasa - 18,000 lawashi - 1,000 Kasuwar garin Mashi,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - 47,000 sabuwa - 37,000 2- Buhun Dawa - 41,000 3- Buhun Gero - 39,000 4- Buhun Kalwa - 32,000 5- Buhun Sobo - 35,000 6- Buhun wake - 44,000 7- Buhun waken suya - 42,000 8- Buhun tattasai - 5000 9- Buhun Tumatur kauda - 11,000 10- Buhun Aya kanana - 37,000 manya - 41,000 11 Buhun Barkono - 31,000 12- Buhun Dankali - 15,000 13- Buhun Lalle - 13,000 Kasuwar garin funtua, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 52,000 sabuwa - 28,000 _ 30,000 2- Buhun Dawa - 3- Buhun Gero - 40,000 4- Buhun Dauro - 5- Buhun Shinkafa - 78,000 samfarera - 24,000 6- Buhun Wake - 55,000 sabo - 44,000 7- Buhun Waken Suya 8- Kwandon Tumatur- 2,500 9- Buhun Tarugu - 9,000 10- Buhun citta - 32,000 Daga Aysha Abubakar Danmusa

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050