Labarai

Gwamna Raɗɗa Ya Sauke Shugaban Hukumar Tattara Haraji Ta Jihar Katsina

Gwamna Raɗɗa ya sauke shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya cire sabon shugaban hukumar tattara haraji ta jihar. Wannan da na kunshe ne a cikin wata takardar da aka aikawa shugaban hukumar ranar Litinin, 19 ga watan Satumba, 2023 daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar. A cikin takardar, an bayyana cewa an cire shugaban hukumar ne biyo bayan janye tantancewar da majalisar dokokin jihar Katsina ta yi ma shi a kwanan baya. Mai karatu zai iya tuna cewa a kwanan baya ne Gwamnan ya tura sunan Prof Sani Mashi majalisar dokokin jihar Katsina domin su tantance shi a matsayin shugaban hukumar tattara haraji ta jihar. Bayan sun tantance shi, daga baya kuma sai majalisar ta ce ta gano wasu kurakurai a tattare da shi wanda kuma suka janye tantancewar da suka yi masa.

Majalisa Ta Buƙaci A Rufe Wurin Sharholiya Na Luna Otel Din-din-din Dake Garin Katsina

Majalisa ta buƙaci a rufe wurin sharholiya na Luna Otel din-din-din dake garin Katsina Majalisar dokokin jihar Katsina ta nemi Gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki matakin gaggawa na rufe shahararren otel din nan Luna dake a cikin garin Katsina. Ɗanmajalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Ali Abu Albaba shi ne ya gabatar da ƙudirin wanda ya samu goyon bayan illahirin ‘yanmajalisar dokokin. Kamar yadda Katsina Post ta rawaito, yayin gabatar da ƙudirin, ɗanmajalisar ya koka da gudummuwar da otel ɗin ke badawa wajen ɓata tarbiyar yara Mata musamman ƙananan Yara a Katsina. Hon. Albaba ya bayyana cewa Luna ta zama dandalin dake tara ‘yanmata ƙanana, da ake shan barasa da kuma mafaka ga miyagu masu aikata laifuka daban-daban. Haka kuma yace akwai sauran wuraren sharholiya dake a cikin garin Katsina waɗanda ya kamata Gwamnati ta rufe bisa ayyukan assha da akeyi da suka saɓa dokokin jihar. Yayi tuni ga zauren a kan dokar da ‘yanmajalisar suka yi na hana sha da sai da giya da wasu manyan laifuka a jihar wanda a cewar shi, Otel din Luna na ɗaya daga cikin wuraren da ake aiwatar da hakan. Hon. Albaba ya kara da cewa mafi yawancin masu buɗe wuraren ba ‘yan jiha ba ne kuma suna taimakawa wajen gurɓata tarbiyar ‘yan jihar Katsina. Ya roki zauren majalisar ya amince a tura ma ɓangaren zartarwa buƙatun majalisar domin a ɗauki matakin rufe otel din baki ɗaya.

Yadda Jerin Farashin Abinci Yake Yau Laraba A Wasu Kasuwannin Jihar Katsina.

Yadda jerin farashin Abinci yake yau Laraba a wasu Kasuwannin jihar Katsina. Kasuwar garin Ingawa,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 48,000 sabuwa - 39,000 2- Buhun Dawa - 35,000 Mori - 39,000 Fara - 34,000 3- Buhun Gero - 39,000 4- Buhun Maiwa - 38,000 5- Buhun Shinkafa - 76,000 shenshera - 25,000 6- Buhun Gyada - 59,500 Mai bawo - 25,000 7- Buhun Wake kana - 32,000 manya - 44,000 sabo - 31,000 8- Buhun Waken Suya - 33,000 9- Buhun Alabo - 38,000 10- Buhun Tarugu - 28,000 11- Buhun Dankali - 9,000 Kasuwar garin Danmusa, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 42,000 2- Buhun Dawa - 52,000 3- Buhun Gero - 37,000 4- Buhun Dauro - 49,000 4- Buhun Shinkafa - 68,000 Shanshera - 29,000 5- Buhun Gyada - 74,000 Mai bawo - 26,000 6- Buhun Waken suya - 38,000 7- Buhun Wake - 44,000 8- Buhun Aya - 43,000 kanana - 38,000 9- Buhun Alabo - 27,000 10- Buhun Tattasai - 23,000 11- Kwandon Tumatur - 5,600 12- Buhun Tarugu - 8,800 13- Buhun Dabino - 85,000 14- Buhun Barkono - 22,000 15- Buhun Dankali - 14,000 16- Buhun Albasa - 22,000 17- Buhun Tsamiya - 16,000 Kasuwar garin kankara, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 45,000 sabuwa - 32,000 2- Buhun Dawa - 42,000 3- Buhun Dauro - 42,000 4- Buhun Gyada - 75,000 5- Buhun Wake - 50,000 Sabo - 40,000 6- Buhun Waken suya - 32,000 7- Buhun Garin Kwaki - 28,000 8- Buhun Alabo - 42,000 9- Buhun Albasa - 20,000 10- Buhun Barkono - 20,000 Kasuwar garin Ajiwa a Karamar Hukumar Batagarawa, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - 37,000 2- Buhun Dawa - 45,000 3- Buhun Gero - 39,000 4- Buhun Gyada - 71,000 5- Buhun wake - 50,000 6- Buhun waken suya - 42,000 7- Buhun Alabo - 35,000 8- Buhun Albasa - 19,000 9- Buhun Dankali - 18,000 10- Buhun Barkono - 37,000 11- Buhun Garin Kwaki - 25,000 Kasuwar garin Bakori,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - sabuwa - 30,000 2- Buhun Dawa - 41,000 3- Buhun Gero - 54,000 sabo - 30,000 4- Buhun Dauro - 60,000 5- Buhun Alabo - 40,000 6- Buhun Gyada tsaba - 75,000 mai bawo - 23,000 7- Buhun Shinkafa tsaba - 70,000 shanshera - 28,000 8- Buhun Wake - 36,000 sabo - 46,000 9- Buhun waken suya - 38,000 10- Buhun Barkono - 37,000 11- Buhun Dankali - 16,000 12- Kwandon Tumatur - 2,000 kauda - 15,000 13- Buhun Tarugu - 21,000 14- Buhun Albasa - 26,000 lawashi - 1,800 Kasuwar garin Mashi,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara - 44,000 sabuwa - 36,000 2- Buhun Dawa - 40,000 3- Buhun Gero - 34,000 4- Buhun Kalwa - 40,000 5- Buhun Sobo - 35,000 6- Buhun wake - 44,000 7- Buhun waken suya - 43,000 sabo - 36,000 8- Buhun tattasai - 40,000 9- Buhun Tumatur kauda - 19,000 10- Buhun Aya kanana - 38,000 manya - 47,000 11 Buhun Barkono - 18,500 12- Buhun Dankali - 15,000 13- Buhun Lalle - 13,000 Kasuwar garin funtua, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 52,000 sabuwa - 32,000 2- Buhun Dawa - 44,000 3- Buhun Gero - 34,000 4- Buhun Dauro - 5- Buhun Shinkafa - 76,000 samfarera - 25,000 6- Buhun Wake - 48,500 7- Buhun Waken Suya - 38,000 tsoho - 45,000 8- Buhun Tattasai - 9- Kwandon Tumatur- 2,500 10- Buhun Tarugu - 9,000 11- Buhun citta - 44,500 12- Buhun taki Yuri - 20,700 Daga Aysha Abubakar Danmusa.

Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta ƙirƙiro Wutar Lantarki A Wasu Asibitocin Jihar

Gwamnatin jihar Katsina za ta ƙirƙiro Wutar Lantarki a wasu asibitocin jihar Kwamishina lafiya na jihar Katsina yace a shirye-shiryen da Gwamna Raɗɗa yake don haɓɓaka kiwon lafiya a jihar, zai ƙirƙiro wutar lantarki domin bada wuta a wasu Asibitocin jihar Katsina nan da shekara mai zuwa. Kwashinan lafiya na jihar Katsina Dr. Bashir Gambo Saulawa shi ne ya bayyana haka a yayin kaddamar da kayayyakin gwaje-gwaje na cutar sida a Katsina wanda suka kaddamar tare da shugaban hukumar KATSACA Dr. Bala Nuhu Kankiya Sadaukin Kankia, a ranar Talata 19 ga watan Satumba 2023. Katsina Post ta samu cewa, daga cikin kayayyakin ayyuka a Asibitoci 347 dake faɗin jihar za a dauki wasu Asibitocin domin saka su cikin jerin waɗanda za a samar ma da wuta ta musamman don saka manyan kayan aikin da za a rinƙa gudanar da ayyukan kiwon lafiya ba sai an fita wata jiha ba. Kwashinan lafiyar yace Malam Dikko Umaru Raɗɗa yana nan a kan bakansa gameda samar da kayan ayyuka na zamani a ɓangaren kiwon lafiya a jihar Katsina, yace za su jajirce don ganin sun sauke nauyin da aka ba su a kowanne bangare a ma'aikatar kiwon lafiya.

Allah Ya Yi Ma Ɗanmasanin Kaita Rasuwa

Allah ya yi ma Ɗanmasanin Kaita rasuwa Ɗanmasanin Kaita, Malam Mustapha Dankama Allah ya yi ma sa rasuwa a Katsina Sheikh Mustapha Yusuf Dankama, wanda shi ne Ɗanmasanin Kaita Katsina Post ta samu rasuwar sa. An gudanar da jana'izarsa da misalin karfe 5:00 na yammacin Litinin 18 ga watan Satumba 2023 a gidansa dake Unguwar Taƙwiƙwi, Dankama a yankin ƙaramar hukumar Kaita dake jihar Katsina. Al'umma daban-daban ne sukai addu'a a gareshi a kan Allah ya yikansa da Rahama.

Yadda Farashin Abinci Yake Yau Litinin A Wasu Kasuwannin Jihar Katsina

Yadda farashin Abinci yake yau Litinin a wasu Kasuwannin jihar Katsina Kasuwar garin Dandume, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara fara - 54,000 ja sabuwa - 35,000 sabuwa - 32,000 2- Buhun Dawa - 47,000 3- Buhun Gero - 37,000 4- Buhun Dauro - 37,000 5- Buhun Dabino - 82,000 6- Buhun Wake - 65,000 ja - 62,000 sabo - 47,000 7- Buhun waken suya - 34,000 8- Buhun Aya - 50,000 kanana - 42,000 9- Buhun Gyada tsaba- 82,000 ja - 95,000 mai bawo - 22,000 10- Buhun Shinkafa tsaba - 73,000 shanshera - 31,000 ta tuwo - 82,000 11- Buhun Kalwa - 45,000 wankakka - 55,000 12- Buhun Dankali - 12,000 13- Buhun Tattasai solo - 6,000 kauda - 40,000 14- Buhun Albasa - 20,000 15- Buhun Kubewa busassa - 30,000 Kasuwar garin Dutsi , ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 53,000 ja - 54,000 Sabuwa - 40,000 2- Buhun Dawa mori - 42,000 fara - 36,000 3- Buhun Gero - 40,000 4- Buhun maiwa - 40,000 5- Buhun Wake - 43,000 ja - 34,000 sabo - 41,000 6- Buhun Waken suya - 39,000 7- Buhun Shinkafa - 76,000 shanshera - 25,000 8- Buhun Gyada tsaba - 62,000 mai bawo - 27,000 9- Buhun Kalwa - 31,000 tsohuwa - 40,000 10- Buhun Alabo - 33,000 11- Buhun Aya kanana - 32,000 manya - 39,000 12- Buhun Dankali - 12,000 Kasuwar garin Mai'adua, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara Sabuwa - 38,000 2- Buhun Dawa - 52,000 3- Buhun Gero - 33,000 4- Buhun Gyada - 67,000 Mai bawo - 25,000 5- Buhun Shinkafa tsaba - 65,000 shanshera - 32,000 6- Buhun Wake - 46,000 7- Buhun waken suya - 41,000 8- Buhun Alabo - 45,000 9- Buhun Tarugu ja - 17,000 10- Buhun Garin kwaki - 22,000 ja - 25,000 11- Buhun Dankali - 18,000 12- Buhun Makani - 13,000 Kasuwar garin 'Yantumaki a karamar hukumar Danmusa,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun masara tsohuwa -40,000 Sabuwa - 34,000 2- Buhun Dawa - 36,000 3- Buhun Gero tsoho - 43,000 sabo - 40,000 4- Buhun Gyada tsaba - 77,000 mai bawo - 20,000 5- Buhun Shinkafa tsaba - 88,000 shanshera - 28,000 6- Buhun Wake - 52,000 sabo - 48,000 7- Buhun waken suya - 37,000 8- Buhun Alkama - 44,000 9- Buhun Kalwa - 28,000 10- Buhun Tattasai solo - 13,000 11- Buhun Tarugu solo - 20,000 12- Buhun Albasa - 18,000 13- Kwandon Tumatur - 10,000 Kasuwar garin Rimaye a karamar hukumar Kankiya,ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara -50,000 sabuwa - 46,000 2- Buhun Dawa ja - 36,000 fara - 48,000 3- Buhun Gero sabo - 32,000 4- Buhun Dauro - 44,000 5- Buhun Kalwa - 24,000 6- Buhun Shinkafa - 84,000 Shanshera - 24,000 7- Buhun Gyada - 67,000 Mai bawo - 28,000 8- Buhun wake - 48,000 9- Buhun waken suya - 38,00 10- Buhun Barkono - 32,000 11- Buhun Dabino - 90,000 12- Buhun Dankali - 23,000 13- Buhun Tattasai - 55,000 14- Buhun Tarugu solo - 16,000 15- Kwando Tumatur kauda - 47,000 16- Buhun Dabino - 95,000 Kasuwar garin Charanci, ga yadda farashin sa yake kamar haka; 1- Buhun Masara - 50,000 Sabuwa 35,000 2- Buhun Dawa - 32,000 3- Buhun Gero - 46,000 4- Buhun Shinkafa - 67,000 5- Buhun Alabo - 40,000 6- Buhun Wake sabo - 46,000 tsoho - 50,000 7- Buhun Waken suya - 35,000 8- Buhun Tattasai - 15,000 9- Kwandon Tumatur - 4,000 10- Buhun Tarugu - 14,000 11- Buhun Albasa - 20,000 12- Buhun Dankali - 10,000 13- Buhun Alkama - 55,000 Daga Aysha Abubakar Danmusa

An Tsige Sarkin Kurayen Katsina, Hakimin Kuraye Daga Sarautar Shi

An tsige Sarkin Kuraye, Hakimin Kuraye daga sarautar shi Masarautar Katsina ta tsige Alhaji Abubakar Abdullahi Amadou daga sarautar shi ta Sarkin Kurayen Katsina, Hakimin Kuraye. Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwar da sakataren masarautar Katsina, Sarkin Yaƙin Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo ya sanya ma hannu. Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnatin jihar Katsina ce ta bada umarnin tsige hakimin daga sarautar shi. Ga wasiƙar da masarautar ta aikewa hakimin: YI MAKA RITAYA DAGA SARAUTAR SARKIN KURAYEN KATSINA, HAKIMIN KURAYE: Bisa ga Takardar da Majalissa Mai-Martaba Sarkin Katsina Alh. (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman CFR, ta samu daga Offishin Sakataren Gwamnati mai lamba KTS/SGS/SEC.54/T/7 ta ranar 15/9/2023, akan maganar Daura Auren Alh. Lawal Mamman Auta da Hajiya Halimatu Abdullahi Kuraye, wadda Gwamnatin Jiha ta bada umurnin Yi maka Ritaya daga Sarautar Sarkin Kurayen Katsina. Don haka, Masarautar Katsina ta yi maka Ritaya daga Sarautar Sarkin Kurayen Katsina daga Yau Litinin 18/9/2023. Da fatan Allah Ya bamu lafiya da zama lafiya amin.

Maidabino Investment