Sadiq Bindawa
July 27, 2022 - 02:55:14 pm
A ce ni ne shugaban Ƙasa!
Zan rufe Hedkwatocin shugabannin tsaron ƙasar nan kaf, Tun daga Kan NPF, Land Army, AIR Force, Navy, NCS, NIS, DSS, NIA da suke à Abuja, domin shan AC, da aikin biro da takarda ya ƙare.
Zan mayar da hedkwatocinsu, wucin gadi a dazukan jihohin da Tsaro ya fi ƙamari, Katsina, Zamfara, Kaduna, Sokoto, Maiduguri da Niger.
Za a raba su, kashi kashi, Rukunin rukuni, runduna runduna, da za su bi lungu da saƙo, kwazzabai, da ƙoramu, duwatsu da tsaunika, sarƙaƙiyya da duhuwa, itace da ciyawu, na duk wasu dazuka da ake zargin maboyar Ƴan taddace. Su fita neman su, ruwa jallo, su ka she kowa.
NIA da DSS su Nemi bayan sirri, ta amfani da surveillance security drones, divices antennas, motion didactors.
Su kuma Sojoji da haɗin guiwar Jami'an Tsaro, suna amfani da bayanan su, su yi RUTHLESS OPERATIONS akan su.
Babu wanda zai dawo Abuja ofis, aikin biro da takarda har sai an ƙarar da duk wasu Ƙungiyoyi na ta'addanci a yankin Arewa da Nijeriya.
Jami'an da ba sa iya yaƙi, saboda nauyin jiki, ko ƙiba, zan masu ritiya, domin buɗewa sabon jini hanyar samun aiki. Idan kuma suna da ƙwarewa ta wani bangaren za a tafi da su.
Duk wasu sojoji da Jami'an tsaro da ke Barracks, da waɗanda aka tura wasu Ƙasashe aikin Kwantar da tarzoma, zan bayar da umarni a dawo da su gida.
Zan bayar da umarni, Duk wasu Ƴan ta'adda da aka kama, a jera su, a harɓe nan take, sannan à yi Video à sakawar kafofin yaɗa labarai, Domin ya zama izina ga na baya.
Waɗanda kuma suka miƙa wuya, ko surrender, za ayi masu hukunci na abin da ya dace da su. Ma fi sauƙi shi ne, Poison Injection.
Zan umarci, Hukumar National Emergency Management Agency (NEMA) da Federal Ministry of Humanitarian Services Disaster Management and Social Development. Su riƙa samar da camp-camps à dazukan da ake farautar yan ta'adda, tare da kai abinci da ruwa, ga Sojoji da Jami'an dake bakin daga à kullum.
Duk rana, zan kai ziyara sansanonin Sojoji da jami'an tsaron haɗin guiwar dake fagen daga, domin ƙarfafa masu guiwa, tare da jin matsalolin su, musamman na ƙananan jami'ai.
Zan sa hannu, à takarda, duk Jami'i ko Sojan da ya mutu a wurin wannan aiki, gwamnati zata biya Diya, kuma zata ɗauki nauyin karatun ya'yan sa, tare da ba Iyalan sa Muhalli.
Wannan aikin da zan yi,.. Zai nunawa Yan Ta'addan cewa, gwamnati tamkar jirgin ƙasa ce mai gudu, duk abin da ya tsaya a gabanta, sai ta buge ta wuce. Kawai kyale su akai, da har suke ɗaga yatsa.
Muhammad Cikingida 🗞️