Katsina Post Hausa

Sarkin Katsina Zai Dawo Gida Bayan Shafe Watanni Yana Jinya A Kasar Ingila

Mai Martaba Sarkin Katsina Na Dab Da Dawo Wa Gida Najeriya Bayan Duba Lafiyar Shi A Kasar Waje Sarkin Katsina zai dawo gida bayan shafe watanni yana jinya a kasar Ingila Majalisar Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman Ta Fitar Da Sanarwar Cewar Sarkin Katsina Zai Dawo Gida Najeriya A Ranar Lahadi Mai Zuwa 30 Ga Watan Oktoba, 2022 Daga Kasar Burtaniya Da Ya Je Domin Duba Lafiyarsa. Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Mai Taken Dawowar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman Daga Ƙasar Waje, Wadda Alhaji Sule Mamman Dee, Sarkin Tsaftar Katsina Ya Sanyawa Hannu A Madadin Majalisar. Kamar Yadda Ta Nuna Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman Zai Dawo Najeriya A Ranar 30 Ga Watan Oktoba Daga Birnin London, Inda Zai Sauka Abuja. Ranar Litinin Mai Martaba Sarkin Zai Sauka Filin Sauka Da Tashin Jiragen Sama Na Malam Umaru Musa Yar'adua Dake Katsina Kuma Za'a Gudanar Da Addu'oin Na Musamman Na Allah Ya Kara Wa Sarki Lafiya. Allah Ya Maido Su Lafiya Ya Kara Wa Sarki Lafiya!

An Shawarci Gwamnati Ta Bude 'bankin Nono' A Jihar Katsina

An Shawarci gwamnati ta bude 'bankin nono' a jihar Katsina Masu ruwa da tsaki sun buƙaci Gwamnatin Jihar Katsina data samar da wurin hada hada da shayar da nonon uwa ga yara kanana marayu da suka rasa mahaifan su domin ingantacciyar lafiyar su. Iyan Katsina, Hakimin Mashi, Alhaji Kabir Aminu ne bayar da wannan shawarar da yake jawabi a wurin taron gangamin wayar da kan al'umma kan muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zallah a ranar Alhamis a garin na Mashi. Gangamin dai gidauniyar tallafawa yara ta majalisar dinkin duniya da hukumar lafiya a matakin farko suka shirya shi domin yin bikin makon shayar da nonon uwa ga jarirai na duniya. Da take jawabi, Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina Hajiya Zakiyya Aminu Bello Masari tayi kira ga Iyaye mata dasu tabbatar suna shayar da ƴaƴan su Nono da zaran sun haife su, sun zo Duniya. Hajiya Zakiyya Aminu Bello Masari wadda ta samu wakilcin Babbar Sakatariya ta Ma'aikatar Ƙasa da Sufiyo Hajiya Halima Lawal Usman, tace wannan bikin Shayarwar Nonon uwa yazo akan lokaci. "Dole mu fahimci cewa Shayarwar Nonon uwa dole ake fara yiwa Jariri shi na tsawon watanni 6 tare da ganin an tallafi dukkanin Mata da zaran sun haihu domin a tabbatar sun sha Nonon uwa. "Dole mu fahimci cewa, Shayarwa bawai mahimmancin ga yaro yake ba, har da uwa, da iyalai dama Al'umma baki ɗaya. A nashi jawabin, Shugaban Hukumar kula da Lafiya a matakin Farko Dr. Shamsuddeen Yahaya yace Nonon uwa kashi 80 ruwa ne. Dr. Shamsuddeen Yahaya wanda ya samu wakilcin Darakta ta Hukumar Kula da Lafiya Dr. Nafisa Sani, ya ce yaran da ba'a shayar dasu Nonon uwa ba, sun fi fuskantar barazanar mutuwa a farkon rayuwar su ba kamar wanda aka shayar dashi ba.

A Ce Ni Ne Shugaban Ƙasa Ga Hanyoyin Da Zanbi In Daƙile 'yan Bindiga- Daga Muhammad Cikingida

A ce ni ne shugaban Ƙasa! Zan rufe Hedkwatocin shugabannin tsaron ƙasar nan kaf, Tun daga Kan NPF, Land Army, AIR Force, Navy, NCS, NIS, DSS, NIA da suke à Abuja, domin shan AC, da aikin biro da takarda ya ƙare. Zan mayar da hedkwatocinsu, wucin gadi a dazukan jihohin da Tsaro ya fi ƙamari, Katsina, Zamfara, Kaduna, Sokoto, Maiduguri da Niger. Za a raba su, kashi kashi, Rukunin rukuni, runduna runduna, da za su bi lungu da saƙo, kwazzabai, da ƙoramu, duwatsu da tsaunika, sarƙaƙiyya da duhuwa, itace da ciyawu, na duk wasu dazuka da ake zargin maboyar Ƴan taddace. Su fita neman su, ruwa jallo, su ka she kowa. NIA da DSS su Nemi bayan sirri, ta amfani da surveillance security drones, divices antennas, motion didactors. Su kuma Sojoji da haɗin guiwar Jami'an Tsaro, suna amfani da bayanan su, su yi RUTHLESS OPERATIONS akan su. Babu wanda zai dawo Abuja ofis, aikin biro da takarda har sai an ƙarar da duk wasu Ƙungiyoyi na ta'addanci a yankin Arewa da Nijeriya. Jami'an da ba sa iya yaƙi, saboda nauyin jiki, ko ƙiba, zan masu ritiya, domin buɗewa sabon jini hanyar samun aiki. Idan kuma suna da ƙwarewa ta wani bangaren za a tafi da su. Duk wasu sojoji da Jami'an tsaro da ke Barracks, da waɗanda aka tura wasu Ƙasashe aikin Kwantar da tarzoma, zan bayar da umarni a dawo da su gida. Zan bayar da umarni, Duk wasu Ƴan ta'adda da aka kama, a jera su, a harɓe nan take, sannan à yi Video à sakawar kafofin yaɗa labarai, Domin ya zama izina ga na baya. Waɗanda kuma suka miƙa wuya, ko surrender, za ayi masu hukunci na abin da ya dace da su. Ma fi sauƙi shi ne, Poison Injection. Zan umarci, Hukumar National Emergency Management Agency (NEMA) da Federal Ministry of Humanitarian Services Disaster Management and Social Development. Su riƙa samar da camp-camps à dazukan da ake farautar yan ta'adda, tare da kai abinci da ruwa, ga Sojoji da Jami'an dake bakin daga à kullum. Duk rana, zan kai ziyara sansanonin Sojoji da jami'an tsaron haɗin guiwar dake fagen daga, domin ƙarfafa masu guiwa, tare da jin matsalolin su, musamman na ƙananan jami'ai. Zan sa hannu, à takarda, duk Jami'i ko Sojan da ya mutu a wurin wannan aiki, gwamnati zata biya Diya, kuma zata ɗauki nauyin karatun ya'yan sa, tare da ba Iyalan sa Muhalli. Wannan aikin da zan yi,.. Zai nunawa Yan Ta'addan cewa, gwamnati tamkar jirgin ƙasa ce mai gudu, duk abin da ya tsaya a gabanta, sai ta buge ta wuce. Kawai kyale su akai, da har suke ɗaga yatsa. Muhammad Cikingida 🗞️

Tarihi Da Nasarorin Dr. Mohammed Barau Tanimu, Ɗantakarar Gwamnan Katsina Ƙarƙashin Jam'iyyar Accord

Tarihi da Nasarorin Dr. Mohammed Barau Tanimu, Ɗantakarar Gwamnan Katsina Ƙarƙashin jam'iyyar Accord An haifi Dr. Mohammed Tanimu Barau ranar 4 ga watan febreru a shekara ta1963 a Katsina, Unguwar tsohuwar Kasuwa Kusada Dan-marina. ILLIMI DA MAKARANTUN DA YA JE Mohammed Tanimu Barau ya faro karatunsa ne a makarantar Firamare ta Rafindadi da ke a cikin Katsina, tsakanin shekarun 1970-76, sa'anan ya shiga makarantar sakandaren ta Government Secondary school Funtua a shekarar 1976-1981. Ya samu kwarewa ta fannin harka ta kididdigar gidaje da gudanarwa (quantity surveying and project management) daga koyarwa zuwa zane - zane, da gine ginen gidaje da offisoshi amakarantun Katsina Polytechnic Katsina da Kaduna Polytechnic, Kaduna tun daga shekarar 1982 zuwa 2003. TARIHIN WURAREN AIKI DA NASARORIN DA YA SAMU Dr. Mohammed Tanimu Barau ya shiga harkokin gine - ginen manyan ayyuka tun daga farko har zuwa karshen gini na manyan offisoshi, gidaje, asibitochi, kasuwanni, da suka suka hada da sabbi da kuma gyare gaye, kuma sun shafi na gwamnati, masanantu da kuma wasu dai daikon mutane wanda kudadensu su kai kimanin billion hamsin N50 billion ($424 million) ko sama da haka. Wa annan su suka kawo mashi kwarewa ga harkokin masanantar gine - gine. Kuma ya samu kafa nashi kamfanoni irinsu: 1. BOQ Associates Limited 2. Tanbashe Global Ventures Limited 3. MBT Resources Limited 4. Precious Steel company Ya kuma chigaba da rike mukamai daban daban na iko, (Management) da zama dan kungiyoyi hadda masu zaman kansu kamar Universal peace Federation wadda ta bashi jakada na zaman lafiya na duniya (International Peace Ambassador), Ya kuma rubuta kasidu da bayanai akan alamurra daban daban. Achikin kokarin shin na kyautata wa alumma da kuma kasa-ta ya kirkoro kuma ya zama shugaban gidauniyar ISLAND SURVIVE FOUNDATION, tun bayan registar anyi ayyuka da dama na tallafi da kyautata rayuwa na bayin Allah, kamar su tallafawa kungiyoyin marayu, gajiyayyu da yan gudun hijira. Sauran sun hada da gyaran idon. Acikin aikace-aikacen gidauniyar har da wayarwa matasa kai, da samar masu sanaoi da ayyukan yi wanda sun hada da (N- Power, NIRSAL Finance loans, Survival Funds, Jaiz Bank Loans) shiga aiki Peace corps da dai sauransu. TAKARDUN KWAREWA TA KUNGIYOYI: - Nigerian Institute Of Quantity Surveyors (MNIQS), - Registered Quantity Surveyor (QSRBN). - Institute Of Management Consultant (MIMC) SAURAN TAKARDU NA GIRMAMAWA DA YA SAMU - Honorary Doctor Degree (European American University) - MD/CEO BOQ Associates Limited (Consultancy Firm), - Founder/ Chairman Island Survive Foundation - Patron, Peace Corps Of Nigeria, Katsina State

Gwamna Masari Ya Dauki Nauyin Kiristoci 28 Zuwa Aikin Ibadar Su A Kasar Isra'ila

Gwamna Masari ya dauki nauyin kiristoci 28 zuwa aikin ibadar su a kasar Isra'ila Gwamatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta dauki nauyin zuwa aikin ibadar kiristoci 'yan asalin jihar Katsina kimanin su 28. Kamar yadda Katsina Post ta samu, kiristocin wadanda suka fitowa daga sassa daban daban na jihar za su je kasar Isra'ila ne da kasar Jordan domin ziyarar wuraren ibadar su da kuma wuraren tarihi masu muhimmanci a addinin su. Da yake karin haske a kan batun ga majiyar mu, mai baiwa Gwamna shawara akan addinin kiristocin, Rabaran Ishaya Jimrau, ya bayyana cewa mutanen da gwamnatin ta dauki nauyi sun hada da jami'an gwamnati, malaman addinin kiristocin da kuma shugabannin su na majami'u daban-daban. Rabaran Ishaya ya kuma kara da cewa wasu kiristocin su 28 daga jihar sun biya ma kan su kudin zuwan kuma da su za'a tafi. Daga karshe sai ya godema Gwamnan tare da shan alwashin za su cigaba da bayar da cikakken goyon bayansu ga cigaban gwamnatin a dukkan matakai.

Shekaru 23 Da Rasuwar Shata: Ga Wasu Tambayoyi 7 Da Aka Yi Ma Sa Da Amsoshin Su

Shekaru 23 Da Rasuwar Shata: Ga Wasu Tambayoyi 7 Da Aka Yi Ma sa Da Amsoshin Su Mamman Shata wani shahararren mawakin Hausa ne wanda har duniya ta nade ba lallai za’a sake yin kamarsa ba. Haifaffen Musawa ne ta jihar Katsina amma ya yi kaura zuwa birnin Kano. Lokacin da ya rasu an birneshi a Daura kamar yadda ya bar wasiyya. Yana da wakoki wanda bicike har yanzu bai san yawan su ba dan shi kan sa an tambaye shi ko yasan adadin wakokin da yayi sai amsa dacewa bai saniba amma a shekarun baya an sami wata baturiya ta zo ta hada wakokin sa kimanin dubu hudu. Yanada da abin mamaki kwarai da gaske yakanyi waka duk lokacin da aka bida yayi hakan batareda inda-inda ba. An tambayi Marigayi Dr. Mamman Shata cewar a ina ya soma waka sai ya kada baki ya ce: “A nan Musawa inda aka haife ni a nan na soma waka kuma duk inda na je yawo to da wakata suka ganni. Ko wane dalili ya sa Dr. Mamman Shata ya soma waka a rayuwar sa? Dalili shine kiriniya ta yarinta kurum, bawai don gadon uwa ko uba ba, domin kuwa na dade ina yi bana kabar ko anini, in ma an samu kudi sai dai makada da maroka su dauka. Sai daga baya bayan na mai da waka sana’a na fara amsar kudi. Shin waya sawa Dr. Mamman Shata wannan suna nasa wato Shata? “Wanda ya sa mini wannan suna Shata sunansa Magaji Salamu, shine ya samin suna Shata Mijin mai daki, ita mai dakin kaka ta ce, ita ce ta haifi wanda ya haife ni. Da aka tambayi Dr. cewar wace waka ce ta fi suna kuma ya fi jin dadin ta ko kuma ta fi birge shi a duk ilahirin wakokin da ya yi, sai ya ba da amsa kamar haka“ To wannan wani abune mawuya ci a wurina kuma kowa yace zai iya ganewa karya yake yi tunda shi shatan bai GANE BA. Bisa al’ada ga yanda mawakan Hausa suke yin wakokin su, akwai waka da suke yi wa kansu da kansu kirari a cikinta wadda aka fi sani da suna Bakandamiya. To shima Marigayi Dr. Mamman Shata bai yi kasa a guiwa ba wajen yi wa kansa irin wannan waka. Daya daga cikin hikimomin da Allah ya baiwa Marigayin shine cewar yana iya kirkirar waka a duk lokacin da yaga dama ko kuma aka bukaci da ya yi hakan. Misali wakar da ya yi ta Dajin-runhu da kuma wakar da ya yi ta Canada Centre a lokacin da ya kai ziyara kasar Amurka. Bisa al’adar Hausa, Mawaka sukan yi wa Mutane Waka, to amma a wani lokaci akan yi wa wakar mummunar fahimta, misali wakar da ya yi ta kusoshin Birni Uwawu da kuma wakar nan ta Na-malumfashi Habu Dan-mama, wanda masu fashin bakin wakoki su ke ganin cewa, wadannan wakoki ya yi sune domin ya nunawa Mutane cewar Yan zamani sun rasa inda za su kama, su basu kama Duniya ba kuma basu kama Lahira ba. To da aka tambayi Dr. cewar shin ko wannan bayani na masu fashin bakin wakoki haka yake sai ya ce “To wannan zance ne irin nasu, shi wanda naiwa ya san abinda na ce, kuma masu ji da basira sun san abinda na ce. Daga cikin dalilan da suka sa Marigayi Dr. Mamman Shata ya ke yiwa Mutane Waka, a kwai kwarewa akan sana’a misali wakar da ya yi ta Bawa Direba. An tambayi Marigayi Mamman Shata, shin waye Bawa direba din nan, kuma mai ya sa ya yi masa waka, kuma da gaske ne dukkanin abubuwan da ya fada a cikin wannan waka ta Bawa Direba, gaskiya ne haka abin yake, sai ya ce “Bawa jankin, shi kam Mutumin Katsina ne, amma a Musawa yai wayo, duk abinda na fadi a wakar Bawa haka yake ban kara masa ba, ban rage masa ba, kuma ko da ni ban fadi ba wani sai ya fadi. Har ila yau Marigayi Dr. Mamman Shata yakan yi wa manyan shugabanni waka, mu samman ma wadanda suka tsayar da adalci, yanci, daidaito da kuma hadin kan al’umma, Misali wakar da ya yiwa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Allah ya ji kansa. Sakamakon wakokin da marigayi Dr. Mamman Shata ya yi domin amfanin Al’umma, ya samu yabo da lambobin girmamawa. Haka kuma Mamman Shata ya dan fada cikin harkokin siyasa inda ma har aka zabeshi matsayin kansila a wata mazaba a karamar hukumar Kankia dake jihar Katsina. Daga Abubakar Ibrahim

Gwamna Masari Ya Sake Nada Jobe Da Mustapha Kanti Matsayin Kwamishinoni

Gwamna Masari ya sake nada Jobe da Mustapha Kanti matsayin Kwamishinoni Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya sa ke mika sunan Hon. Faruq Lawal Jobe da Hon. Mustapha Muhammad Kanti Bello ga majalisar Dokoki ta Jihar Katsina domin tantancesu a matsayin kwamishinoni. A na su bangaren, Majalisar Dokokin ta amince da ranar Litinin mai zuwa 20/06/2022, matsayin ranar da zata tantance sabbin wadanda aka turo mata din. Hon. Faruq Lawal Jobe dai shi ne tsohon Kwaminshinan kasafin kudi da tsare-tsare kafin ya ajiye mukamin sa ya shiga takarar kujerar Gwamnan jihar Katsina. Shi kuma Mustapha Kanti Bello kafin ya ajiye mukaminsa ya nemi takarar kujerar Sanata na shiyyar Katsina ta Arewa, shi ne Kwamishinan Ma'aikatu biyu na raya karkara da kuma Kwamishinan hukumar Kimiyya Da Fasaha. Dukkan su dai sun fadi a takarar da suka shiga a zabubbukan fitar da gwani.

Maidabino Investment