Jami'an Tsaro Sun Kama Wanda Ya Kashe Kwamandan 'yansanda A Yankin Dutsinma
Jami'an tsaro sun kama wanda ya kashe Kwamandan 'yansanda a yankin Dutsinma 'Yan sandan Katsina sun kama ɗaya daga cikin 'yanta'addan da a kwanakin baya suka kashe kwamandan yankunan ƙaramar hukumar Dutsinma, ACP Aminu Umar. Rundunar ‘yansanda a jihar Katsina ta ce ta kama wani ɗanbindiga mai shekaru 30, wanda ake zargin yana da hannu wajen kashe Kwamandan yankin Dutsinma, ACP Aminu Umar. Kamar yadda Katsina Post ta samu, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yansandan jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu shi ne ya bayyana haka a lokacin taron Manema Labarai a ranar Alhamis 14 ga watan Satumba 2023. Yace rundunar ‘yansandan da ke sintiri ta samu galaba a kan ‘yanbindigar ne a wani artabu da suka yi da ta kai ga rasa ransa da na wani jami’i wanda aka fi sani da Sabon Jini, an kama shi ne a ranar 30 ga watan Agusta. Wanda ake zargin ya fito ne daga Ƙauyen Tsaskiya da ke ƙaramar hukumar Safana a jihar Katsina. A cewar rundunar 'yansandan, wanda ake zargi ya kasance cikin jerin sunayen da rundunar 'yansandan ta ke nema ruwa a jallo bisa wasu laifuffuka, kamar satar mutane. Satar shanu da sauran munanan laifuka. ASP Abubakar Sadiq Aliyu yace wanda ake zargin an kama shi ne a lokacin da aka kama shi gameda da laifin yin garkuwa da wani Hussaini Nabara da ke Ƙauyen Kagara a ƙaramar hukumar Dutsinma, inda a nan ne ya tabbatar da faruwar lamarin a yayin zurfafa bincike aka gano shi danƙungiyar wani Abubakar ne mai suna Jankare, wanda fitaccen shugaban ‘yanfashi ne a yankin Dutsinma Tunda farko wanda ake zargin ya amsa laifin haɗa baki da wasu miyagun ‘yanbindiga domin yi wa marigayi ACP Umar kwanton ɓauna a yayin da rundunar ta kama mutum 35 a ranar 2 ga watan Satumba, a yayin da ake gudanar da bincike wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zargin sa da shi. Idan ma su bibiyar labarai ba su manta ba, a ranar 5 ga watan Yuli ne ‘yanbindiga suka yi wa marigayi ACP Umar kwanton ɓauna suka kashe shi, yayin da yake jagorantar tawagar sintiri a aikin da suka saba yi na fatattakar ‘yanta’adda a yankin Dutsinma.