Sports

An Yi Zaman Sulhu Tsakanin Magoya Bayan Katsina United Da Kano Pillars

An yi zaman sulhu tsakanin magoya bayan Katsina United da Kano Pillars Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Katsina United sun kara dankon zumunci a tsakaninsu gabanin gasar kwararru ta kwallon kafa ta Najeriya da ke tafe. Tawagar magoya bayan kungiyar Chanji Boys ta gana da magoya bayan Sai Masu Gida a ranar Lahadi a Kano. Wakilan biyu sun amince kan yadda za a ilimantar da membobi kan yadda za su guje wa tashin hankali a lokacin wasanni da bayan wasannin NPFL. Sun kuma bukaci shugabannin kungiyar da su nemo mafita mai ɗorewa a tsakanin su kafin a fara gasar NPFL. Kano Pillars da Katsina United sun samu karin girma daga kungiyar Northern Conference group ta Najeriya. Majiyar Katsina Post ta Daily Post ta tuna cewa wasu matasa da ake zargin magoya bayan kungiyar Kano Pillars ne suka lalata motar bas din Katsina United bayan sun tashi babu ci a filin wasa na Sani Abacha a shekarar 2022.

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Katsina United, Zata Tantance 'Yan Wasa 120 Dake Katsina

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Katsina United, Zata Tantance 'Yan Wasa 120 Dake Katsina Hukumar gudanarwar ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United Fc ta gayyaci ’yan asalin jihar Katsina 120 domin samun jajirtattun ’yan wasan ƙwallo da suka fito daga ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina. An shirya gudanar da tantance 'yan wasan ƙwallon ne a ranar Laraba 28 ga Satumba zuwa 6 ga Oktoba 2022 a cikin filin wasa na Muhammadu Dikko Katsina, da misalin ƙarfe 10:00 na safe, kamar yadda Katsina Post ta rawaito. Tantancewar da za a yi wa 'yan wasan ƙwallon, hakan na nufin sabunta ƙungiyar ne da kuma bawa 'yan wasan gida dama su shiga a domin a dama da su. A cewar daraktan ci gaban ƙwallon ƙafa na ƙungiyar Saleh Yusuf, yace an bashi sunayen kulub ɗin da suka fi tasiri da iya wasanni a jihar Katsina, wanda a cikinsu ne zasu zaƙulo jajirtattu masu hazaƙa a ƙananan hukumomi 34 a Katsina, kamar yadda Katsina Post ta tattaro. Yace, duk da sun ɗauki aƙalla ɗan wasa 20 da sukayi renansu a ƙungiyar Katsina United, waɗanda 'yan asalin cikin birnin Katsina ne, duk da haka zasu ƙara ɗaukar wasu 'yan wasan ƙwallon idan har suka kasance haziƙai. Daraktan ci gaban ƙwallon ƙafa na ƙungiyar, ya bayyana cewa za a samar da abinci da wurin kwana ga duk ‘yan wasan da aka gayyata. Don haka, an yi kira ga ’yan wasan da aka gayyata da su baje kolin wasannin motsa jiki da kuma biyayya ga na gaba da su, tare da gudanar da atisayen da ya kawosu wurin, kuma za a tabbatar an yi wa kowa adalci ga duk wanda ya cancanci a yi masa rijista da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United. Hukumar gudanarwa ta ƙwallon Katsina United, ta bayyana godiya ga kwamishinan wasanni na jihar Katsina, Dr Bishir Gambo Saulawa da ya baiwa ‘yan wasan gida damar baje kolinsu, sun ce hakan zai ƙara haɓɓaka ƙwazon ‘yan wasa da kuma ci gaban harkar ƙwallon ƙafa a Katsina baki ɗaya.

Katsina United Za Ta Yi Garambawul, Ta Na Gayyatar 'yan ƙwallo Na Gida Su Zo A Gwada Su

A yunƙurin sake fasalin sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United, Hukumar gudanarwar ƙungiyar ta amince da gayyatar 'yan wasan 'yan asalin jihar Katsina da su zo domin a gwada ƙwazonsu. Shugaban kungiyar, Prince Abdul-Samad Badamasi ya ce ’yan wasan da aka gayyata za su yi da 'yan wasan ne domin a gwada hazaƙarsu ta zabar waɗanda suka fi kowa ƙwazo a cikin su a lokacin, kamar yadda Katsina Post ta rawaito. Prince Abdul-Samad Badamasi ya bayyana cewa, za a aika da wasiƙun gayyata ga ƙungiyoyin kwallon kafa daban-daban da ke shiyyar Daura, Funtua, da kuma Katsina ta tsakiya. Ya ba da tabbacin cewa za a yi wa ’yan wasa da suka cancanta rajista da Katsina United, Shugaban ya yi nuni da cewa, za a ƙara wa ‘yan wasan da aka yi rajista ƙarin lokacin wasa a kakar wasa mai zuwa, kamar yadda Katsina Post samu labari. A cewarsa, matakin na nufin ba da dama ga ’yan wasa na Gida don bayar da gudunmawa wajen kawo sauyi ga kulob ɗin jihar Katsina. Don haka, Hukumar Gudanarwar ta umarci Kungiyoyin Ƙwallon Kafa ta Jihar da su yi amfani da damar da suka samu na kasancewa cikin sabuwar ƙungiyar Katsina United, domin nuna kishin jihar.

Gwamnatin Kano Ta Gyara Motar Katsina United Da Magoya Bayan Kano Pillars Suka Lalata

Ganduje Ya Gyara Motar Katsina United Da Magoya Bayan Kano Pillars Suka Lalata Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagoranchin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta gyara motar yan wasan Kungiyar Katsina United da magoya bayan Kano Pillars suka lalata a kwanakin baya. Idan dai za'a tunawa, a lokacin wasa na 23 na gasar Firimiyar Najeriya ta 2021/2022, wasu fusatattun magoya bayan Kano Pillars din suka lalata motar Katsina United din. Bayan hakan ta faru ne Gwamna Ganduje ya sha alwashin gyara motar, kamar yadda Hukumar Tsara Gasar ta NPFL ta bada umarni. Hukumar Kulob din na Katsina United ta godewa Gwamnatin Jihar Kano akan cika wannan alkawari da ta yi, tare da addu'a akan kiyaye faruwar irin wannan lamari. Hukumar kulob din ta ce irin wannan lamari na kawo nakasu ga martabar arewa maso yamma, a sabili da haka sai an kauracewa faruwar irin sa a nan gaba. Horizon News Hausa

NPFL: Ƙungiyar Sunshine Stars Ta Doke Katsina United Da Ci 2-0 A Akure

A ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyar Sunshine Stars FC ta birnin Akure ta sake samun nasara bayan ta doke Katsina United a wasan mako na 30 na gasar cin kofin kwallon kafa ta Najeriya NPFL. Wasan da aka buga a filin wasa na Ondo State Complex, Akure a ranar Asabar, kungiyoyin biyu sun buga babu ci a farkon karawar. Sunshine Stars ta samu nasara a kan Rivers United da ci 1-0 a karshe kuma ta kasa samun maki mafi girma a karawar da Shooting Stars da Akwa United a Akure. Sai dai bayan mintuna 13 da aka tashi ana wasan (minti 58) dan wasan Sunshine Stars Midfielder, Azeez Ajagbe ya farke kwallon da ya ci ta hannun kungiyar. A minti na 80 ne aka ba Sunshine Stars fenariti bayan da mai tsaron gidan Katsina Nwabali Stanley ya taka kafar Sunshine Striker, Donald Ugochuckwu a cikin fili inda dan wasan ya ci kwallo 2-0. Kociyan Katsina United, Bishir Sadauki ya ce kungiyarsa ta gaza

Katsina United Vs Kano Pillars To Be Played On Saturday

Katsina United Vs Kano Pillars To Be Played On Saturday League Management Company LMC has re-arrange Kano Pillars encounter against Katsina United Fc in the ongoing NPFL SEASON 2021/2022. The encounter which is MD 23 of the ongoing season is reschedule from Sunday 17/04/2022 to Saturday 16/04/2022 The two NPFL CLUBS are therefore urged to ensure that all logistics are put in place as required by the LMC The Match is going to be played at Muhammadu Dikko Stadium Katsina the Adopted Home of Kano Pillars (Sai Masu Gida) as confirm from the Club Media Officer Lurwanu Idris Malikawa The release is signed by Katsina katsina United Media Officer Nasir Gide. Nasir Gide M.O.

Gov. Masari Appoints Bature As Secretary For Katsina United FC

Governor Aminu Bello Masari has approved the appointment of Malam Abdulkadir Bature as the New Secretary of Katsina United Football Club This is contained in a PRESS RELEASE signed by the State Director of Sports Nalado Iro Kankia and made available to Media Organizations and social media handles The appointment of Malan Abdulkadir Bature followed the retirement of Malam Sani Tunau after 35 years of selfless service to the state Before his appointment Malam Abdulkadir Bature was the former Secretary of the defunct Spotlight Football Club and currently the welfare Officer of Katsina United Football Club Malam Abdulkadir Bature is a graduate of the renown National Institute For Sports (NIS) Lagos, with 27 years of working experience in Sports Sector In the release the Ministry of Sports and Social Development, State Sports Council and the Management of Katsina United thanked the outgoing Secretary and wish him the best of luck in his future endeavors. Nasir Gide M.O

Maidabino Investment