
Allah ya yi ma Ɗanmasanin Kaita rasuwa
Ɗanmasanin Kaita, Malam Mustapha Dankama Allah ya yi ma sa rasuwa a Katsina
Sheikh Mustapha Yusuf Dankama, wanda shi ne Ɗanmasanin Kaita Katsina Post ta samu rasuwar sa.
An gudanar da
jana'izarsa da misalin karfe 5:00 na yammacin Litinin 18 ga watan Satumba 2023 a gidansa dake Unguwar Taƙwiƙwi, Dankama a yankin ƙaramar hukumar Kaita dake jihar Katsina.Al'umma daban-daban ne sukai addu'a a gareshi a kan Allah ya yikansa da Rahama.
Comments