An Tsige Sarkin Kurayen Katsina, Hakimin Kuraye Daga Sarautar Shi

Masarautar Katsina ta tsige Alhaji Abubakar Abdullahi Amadou daga sarautar shi ta Sarkin Kurayen Katsina, Hakimin Kuraye.

Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwar da sakataren masarautar Katsina, Sarkin Yaƙin Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo ya sanya ma hannu. 

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnatin jihar Katsina ce ta bada umarnin tsige hakimin daga sarautar shi. 

Ga wasiƙar da masarautar ta aikewa hakimin:

YI MAKA RITAYA DAGA SARAUTAR SARKIN KURAYEN KATSINA, HAKIMIN KURAYE:


Bisa

ga Takardar da Majalissa Mai-Martaba Sarkin Katsina Alh. (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman CFR, ta samu daga Offishin Sakataren Gwamnati mai lamba KTS/SGS/SEC.54/T/7 ta ranar 15/9/2023, akan maganar Daura Auren Alh. Lawal Mamman Auta da Hajiya Halimatu Abdullahi Kuraye, wadda Gwamnatin Jiha ta bada umurnin Yi maka Ritaya daga Sarautar Sarkin Kurayen Katsina.

Don haka, Masarautar Katsina ta yi maka Ritaya daga Sarautar Sarkin
Kurayen Katsina daga Yau Litinin 18/9/2023. 

Da fatan Allah Ya bamu lafiya da zama lafiya amin.

Sadiq Bindawa

Writer, Publisher, Blogger, Editor, Director, Photojournalist, Agriculturelist, Media specialist

Follow Me:

Comments