Sa'in Katsina Ya Cika Shekaru 50 Cif A Sarautarsa

Sa'in Katsina Ya Cika Shekaru 50 Cif A Sarautarsa

Maigirma Sa'in Katsina Amadu na Funtua ya cika shekaru 50 cif a sarautar Sa'in Katsina. 

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa a ranar 16 ga watan Satumba a shekarar 1973 ne aka naɗa Alhaji Amadu Na Funtua a matsayin Sa'in Katsina, inda jiya 16 ga watan Satumba 2023 ya cika shekaru 50 cif a bisa Sarautar Sa'in Katsina. 

Kamar yadda Katsina Post ta

samu, Marigayi Sarkin Katsina Alhaji Dr. Usman Nagogo, shi ne wanda ya naɗa Alhaji Amadu na Funtua a shekarar 1973 a matsayin Sa'in Katsina. 

Sa'in Katsina Amadu na Funtua, a yanzu yana da shekaru 94 a duniya wanda yana daga chikin mutanen da suka yi tsawon rai cikin waɗanda aka baiwa sarauta a tun a wancen lokacin. 

Al'umma da yawa ne sukai Addu'ar a gareshi a kan Allah ya ƙara ma shi lafiya da nisan ƙwana.

Zaharaddeen Gandu

Zaharaddeen Gandu

Represent Journalists, Writer, Song-writter, Publisher, Photojournalist, Media specialist.

Follow Me:

Comments