An Kama Wani Kasurgumin Dan Bindiga A Katsina

An kama wani kasurgumin dan bindiga a Katsina 

Rundunar Ƴan Sandan jihar Katsina ta kama wani ƙasurgumin ɗan ta'adda mai suna Saminu Usman ɗan asalin ƙaramar hukumar Jibia, wanda ake zargi da yin garkuwa da mutane.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar a madadin Kwamishinan ƴan sandan jihar.

A cewar ASP Abubakar rundunar a ƙoƙarin ta na yaƙi da ƴan ta'adda da ta'addanci a jihar Katsina, ta samu nasarar cafke wani Saminu Usman mai shekaru 19 ɗan asalin ƙaramar Jibiya da ake zargi da aikata laifin yin garkuwa a ƙauyen tashar Hurera da ke cikin jibiya.

ASP Abubakar

Sadiq ya ƙara da cewa a ranar da akayi garkuwar, an kawo rahoton sace ɗan shekara 5 mai suna Usman Shu'aibu a ofishin ƴan sanda na Jibiya ta hanyar wani Shu'aibu Salisu ɗan asalin garin.

A cewar sa, bayan ya tuntuɓi mahaifin yaron, ya buƙaci a biya shi Naira dubu 600,000.00 da wayar Android guda uku a matsayin kuɗin fansa, wanda uban ya biya ya amso ɗan sa.

ASP Abubakar, ya bayyana cewa, bayan samun rahoton, jami'an rundunar suka bazama neman wanda ya aikata ta'addancin tare da gano shi a garin Lambata na jihar Naija.

Kakakin rundunar yace a lokacin binciken, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin tare da fadin cewar ya haɗa kai wajen ɗauke wani Rabe.

Usman Salisu

Follow Me:

Comments