
Za a kammala aikin titin Jirgin Ƙasan da ya bi ta Katsina zuwa Maradi a shekarar 2025
Ana ci gaba da shirye-shiryen kammala Aikin Titin jirgin kasan da ya taho daga Dawanau a jihar Kano zuwa Daura har cikin Katsina zuwa Maradi.
Ministan sufurin, Alhaji Sa'idu Alƙali ya yi jawabin hakan ne a ranar Jumma'a, lokacin da ya jagoranci ziyarar duba aiki a ma'aikatar.
A cewar sa duk abinda suka zo dubawa sun gani kuma bada jimawa ba za a kammala ayyukan cikin sauki da lumana ba tare da tsangwama ba tare da kuma ƙyayyade ayyukan 'yankwangilar.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, Ministan ya yi bayanin cewa an yi babban aiki wanda idan aka kammala shi zai dade ana amfanarsa bai lalace ba domin ayyukan akwai manufofi ma su kyau.
Yace babbar kwangilar wadda
take a ƙarƙashin jagoranci, Mr. Vadislav Bystreneko, ya ce yarjejeniyar da sukai da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2021 ta kasance kimanin kuɗi dala biliyan 1.95 kuma sun sanya hannu kan ayyukan tare da alƙawarin kammalawa.Alhaji Sa'idu Alkali, ya ƙara da cewa tunda kafin a sake kudin ayyukan, sun ci gaba da wasu manyan ayyuka na zane-zanen, da binciken ƙasa, da kuma kulawa da ayyukan kwangilar.
Daga ƙarshe Mr. Vladislav Byststeko yace gwamnatin tarayya ta kwantar da hankalinta gameda kammala aikin domin sun yanke shawara za su kammala ayyukan a shekarar 2025 domin aikin yana da matuƙar muhimmanci a yankunan Arewa.
Idan baku manta ba, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shi ne ya bada aikin titin jirgin ƙasan tin lokacin shugabancin sa na shugaban kasar Najeriya.
Comments