Za'a Fara Tantance Daliban Da Za'a Ba Tallafin Karatu A Katsina⁩

Hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Katsina ta ce za ta fara bayar da tallafin karatu ga dalibai yan asalin jihar Katsina da suka samu guraben a duk manyan makarantun jihar a ranar 18 ga watan Satumba.

Kakakin hukumar Salisu Lawal Kerau ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Katsina.

Ya ce za a kammala biyan tallafin ne a ranar 9 ga watan Oktoba a manyan makarantu daban-daban na Katsina da kewaye.

Don haka ana

buƙatar duk sabbin ɗalibai su zo tare da kwafin takardar rajista, ko remitta, da ingantaccen katin shaida na makaranta, kafin karɓar shedar samun tallafin.

 Ya bayyana cewa da zarar an fara raba kudaden tallafin, za a fara ba tallafin ga ɗalibai yan asalin jihar Katsina dake a manyan makarantun jihar.

Ya tabbatar da cewa daga baya hukumar za ta cigaba da bada tallafin ga sauran dalibai yan asalin jihar da ke karatu a dukkanin manyan makarantun ƙasar nan.

Sadiq Bindawa

Writer, Publisher, Blogger, Editor, Director, Photojournalist, Agriculturelist, Media specialist

Follow Me:

Comments