
Allah ya yi ma Maigarin Wurma dake yankin Kurfi rasuwa
Alhaji Mustapha Muhammad Ɗandaɗi dake yankin kurfi a jihar Katsina ya rasu.
Maigarin Wurma dake ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Ɗandaɗi Allah ya karɓi rayuwarsa a daren jiya Laraba
13 ga watan Satumba 2023.An gudanar da jana'izarsa da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Alhamis 14 ga watan Satumba 2023 a gidansa dake Unguwar Ƙadangaru dake ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.
Al'umma da dama ne suka yi addu'ar Allah ya jikansa da Rahama.
Comments