An Kama Wani Mutum Da Buhun Alburusai Zai Kai Ma Yan Bindiga A Katsina

An kama wani mutum da buhun alburusai zai kai ma yan bindiga a Katsina 

Jami'an tsaro a jihar Katsina sun daƙile yunƙurin wani matashi bata-gari mai suna Ibrahim Abdullahi, na safarar alburusai zuwa ga yan bindiga a jihar Katsina. 

Kamar yadda Katsina Post ta samu, matashin wanda ya ce shekarun sa 35 a duniya, yana kokarin shigar da alburusan ne zuwa daji wurin yan bindiga

daga kauyen su na Sabon Garin Dunburawa, na karamar hukumar Batsari a Jihar Katsina. 

Da jami'an tsaron ke tuhumar sa, Ibrahim Abdullahi ya ce zai kai wa wani dan bindiga ne mai suna Yusuf alburusan can yammacin garin na Dumburawa bakin lamba. 

Haka zalika bata-garin ya kuma bayyana nadamar sa sannan ya nuna sha'awar sa ta bayar da gudummuwa wajen kamo ɗan ta'addan. 

Mustapha Saddiq

Editor-In-Chief

Simple. Straight forward. Up to date.

Follow Me:

Comments