
Gwamnatin jihar Katsina ta ware Naira biliyan 26.6 wajen magance ambaliyar ruwa da zaizayar Ƙasa a jihar Katsina.
Ya bada tabbacin matakan da gwamnatin ta ɗauka na magance ambaliyar ruwa da zaizayar Ƙasa a jihar.
Hon. Musa Adamu ya jinjina ma Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa da irin kokarin da take na inganta rayuwar al'ummar jihar baki ɗaya.
Katsina Post ta samu cewa hukumar NIMET ta lissafa jihar Katsina a cikin jerin jihohin da zasu fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a Najeriya.
Matakan da gwamnatin ta
ɗauka kamar yanda Kwamishinan ya ambata sun haɗa da samar da shirin kare muhalli guda 13, wayar da kan al'umma akan shirin inganta muhalli, kwashe shara dake kan magudanan ruwa, da kuma ginawa da faɗaɗa magudanan ruwa a jibia.
Kwamishinan yayin da yake tabbatar da ƙudurin gwamnatin Gwamna Dikko Radda na ci gaba da bunƙasa a jihar, ya ce jihar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace da suka haɗa da inganta daji, dashen itatuwa, da kawar da ramuka da sauran su a cikin kwanaki 100 na farko da Gwamnan jihar yayi a ofis.
Comments