An Tsinci Jariri Sabon Haihuwa ƙunshe Da Wasiƙar Mahaifiyar Shi A Katsina

Wasu mutane mazauna unguwar kofar yandaka sun tsinci jariri sabon haihuwa tare da wasiƙa a safiyar yau Litinin.

Katsina Post ta samu cewa an tsinci jaririn ƙunshe cikin tsumma tare da takardar wasiƙa da mahaifiyar ta rubuta dake dauke da saƙonni. 

Kamar yanda rahotanni suka bayyana, a cikin takardar wadda ta haifi yaron ta bayyana cewa ta samu cikin wannan yaron ne ta sanadiyyar fyaɗe da Ƴan Ta'adar Daji sukayi mata tare da kashe Iyayen ta da dangin ta, a cewar ta bata da halin da zata Iya

kulawa da yaron kuma tasan ba kowa bane zai iya ɗaukar nauyin ta da na yaron shi yasa tazo ta ajiye shi ba dan bata son shi ba.

Kazalika, mahaifiyar ta bayyana cewa ta haife shi da misalin ƙarfe Ukku na Daren Yau Litinin.

A halin yanzu dai an samu kimanin Mutane Biyu da duka ce suna Buƙatar a basu yaron zasu raine shi, amma dai Al'umma sun bada Shawarar cewa a fara kai Lamarin ga Jami'an tsaro da kuma Offishin Magajin Garin Katsina kafin a ɗauki wannan matakin, kamar yanda ganau suka tabbatar. 

Sadiq Bindawa

Writer, Publisher, Blogger, Editor, Director, Photojournalist, Agriculturelist, Media specialist

Follow Me:

Comments