
Yan bindiga sun tare motar KTSTA, sun kashe direban, sun tafi da fasinjoji
Labarin da muke samu yana nuni ne da cewa wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun tare motar hukumar sufuri ta jihar Katsina, KTSTA a kan hanyar ta na zuwa Jibia da
rana a ranar Lahadi.Kamar yadda Katsina Post ta samu, yan bindigar sun kashe direban motar sannan kuma sun kwashe fasinjojin cikin motar da ba'a san yawan su ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Cikakken labarin na nan tafe...
Comments