Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Katsina A Fice Daga Jam'iyyar APC

Tsohon mai neman takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar APC a zaben shekarar 2019 Alhaji Garba Sani Dankani Jikan Hambali, ya fice daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar AA (Action Alliance).

Alhaji Garba Sani Dankani ya sanar da ficewar shi daga APC ne a lokacin wani taro da ya gudanar da Ko’odinatocin shi da sauran magoya bayan shi daga Kananan Hukumomi 34 na Jihar Katsina.

A cewar Jikan Hambali, ya fice daga APC ne zuwa AA domin bada gudummuwar shi ga samun nasarar Jam’iyyar a zaben game gari na shekarar 2023 da ke tafe.

Alhaji Garba Sani Dankani ya ce Jam’iyyar AA tana da karfin daukar al’ummar Najeriya ta kai su gachi, ganin nagartar Dan Takarar Shugabancin Kasa na Jam’iyyar wato, Manjo Hamza Almustapha.

Jikan Hambali ya kara da cewar, abinda ya kara mashi kwarin gwuiwa na

shiga Jam’iyyar shine, ganin cewar Dan Arewa ne zai yiwa Jam’iyyar takarar Shugaban Kasa, kuma mutum mai nagarta da zai iya shawo kan matsalolin Najeriya.

Daga nan sai ya bukaci Ko’odinatocin nashi da sauran magoya bayan shi akan su jajirce wurin nemarwa Jam’iyyar goyon bayan jama’a a Kananan Hukumomin su domin ganin an samu nasara a Zaben na 2023.

Alhaji Garba Sani Dankani ya lashi takobin yin duk abinda ya dace domin ganin Dan Takarar nasu Manjo Hamza Almustapha da sauran yan takarar Jam’iyyar sun samu nasara.

Wadanda suka a wurin taron sunyi maraba da chanjin shekar da Jikan Hambali ya yi zuwa Jam’iyyar ta AA.

Sun sha alwashin cewa duk inda Jikan Hambali ya nufa a siyasar shi zasu kasance masu mara mashi baya domin sun gamsu da nagartar shi da manufofin shi na alkairi ga mutanen Jihar Katsina.

Mustapha Saddiq

Editor-In-Chief

Simple. Straight forward. Up to date.

Follow Me:

Comments