
Hadimin Gwamna Masari ya ajiye mukaminsa ya bar APC ya koma NNPP
Mataimaki na musamman ga gwamna Masari na jihar Katsina kan harkokin siyasa Alh Sani Liti 'Yan Kwani ya bar jam'iyyar APC ya koma NNPP.
Sani Liti 'Yan Kwani ya shaida wa
majiyar DCL Hausa ta Blueink cewa ya bar APC yanzu har ma an zabe shi shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Katsina.Yace tuni ya aike da takardar ajiye mukaminsa ga gwamna Masari inda ya ce yana godiya da damar da aka bashi na ya yi wa jihar Katsina hidima.
Comments