
Jami'in kwastam ya kashe wani matashi a Katsina
Wani da ake zargi jami'in hukumar dake hana fasa kwabri ta kwastam ya harbe wani matashi dan Kofar Guda mai suna Abdulmalik Lawal har lahira a jihar Katsina.
Kamar yadda muka samu, lamarin ya auku ne a ranar Asabar, 12/3/2022 da misalin karfe biyar na Yamma.
Kamar yadda muka samu, jami'in kwastam din dai ya harbi Marigayin ne a kokarin sa na ya tsaida su saboda ya gan shi bisa babur tare da abokin
sa dauke da buhu da yayi zargin kayan laifi ne.Sai dai bayan da jami'in kwastam din ya kashe matashin ana dubawa sai aka ga ashe dussa ce sukayi dauko.
Haka zalika Katsina Post ta samu labarin cewa jami'in kwastam din ya yi kokarin guduwa amma jama'ar gari sun kama abokin aikin sa wanda kuma daga baya suka mika shi ga jami'an rundunar yan sanda.
Kawo yanzu dai jami'an kwastam din ba su ce komai ba game da lamarin.
Comments