Za'a sake daukar dakarun tsaron sa kai a ƙananan hukumomi 10 a Katsina
Za'a sake daukar dakarun tsaron sa kai a ƙananan hukumomi 10 a Katsina
- Posted By: Mustapha Saddiq --
- Saturday, 14 Sep, 2024
Za'a sake daukar dakarun tsaron sa kai a ƙananan hukumomi 10 a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta Amince da Fitar da Naira Biliyan Ɗaya da Rabi Domin Ɗaukar Jami'an Tsaron Cikin Gida (Cwatch) Karo na Biyu a Ƙananan Hukumomi Goma, Da Kuma Naira Biliyan Shabiyu da Rabi Domin Siyo Injinan Gwaje-Gwajen Lafiya
Majalisar zartaswa jihar Katsina ta amince da fitar da wan nan zunzurutun Kuɗin ne a ranar Alhamis 12 ga Satumba 2024, a zaman majalisar karo na tara (9th) wanda Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ke jagoran ta.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron majalisar Kwamishinan tsaron cikin gida Dr. Nasir Mu'azu, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina ta amince da fitar da Naira Biliyan Ɗaya da Rabi, domin ɗaukar sabbin jami'an tsaron cikin gida na Cwatch karo na biyu, a ƙanana hukumomi goma na jihar.
Ya bayyana an yanke hukuncin ɗaukar sabbin jami'an tsaron ne domin taimaka ma jami'an da aka ɗauka na farko a ƙananan hukumomi takwas da ke makwabtaka da dazukan da yan ta'addan suke, aan yanke hukuncin sake ɗaukar ne duba da gudummuwar na farkon suka bada ta kimanin kaso talatin na yaƙar yan ta'addan tun bayan ɗaukar su.
Ya ƙara da cewa za'a kashe Kuɗaɗen ne a wajen horas da sabbin jami'an, da kuma samar masu da kayan aikin da ya dace domin fara gudanar da ayyukan su, ƙananan hukumomin da za'a ɗauki jami'an sun haɗa da Dutsin-ma, Kurfi, Charanchi, Musawa, Matazu, Malumfashi, Ɗanja, Kafur, Bakori da kuma Funtua.
Shima da yake magana Kwamishinan lafiya na jihar Katsina Hon. Musa Adamu Funtua, wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren ma'aikatar lafiya ta jiha Ahmed Tijjani, ya bayyana majalisar ta amince da fitar da Naira Biliyan Shabiyu da rabi (12,537,388,500) domin samar da injina guda goma na gwaje-gwajen lafiya a sabuwar cibiyar gwajin lafiya da gwamnatin ke ginawa a asibitin Janar Amadi Rimi, da ke nan cikin Katsina.
Manyan injinan gwaje-gwajen lafiyar sun haɗa da "Maganetic Resonance Imagine MRI 3.0, Cityscan, nuclear Imagine machine, Mammogram, da sauran su".
Ya bayyana tuni aka fara aikin ginin cibiyar gwaje-gwajen lafiyar, wanda idan aka kammala aikin zata zama irin ta ta farko a faɗin Afirka ta yamma, kuma zata taimaka ƙwarai wajen gano da dama na cutukan dake damun al'umma.