Yansanda sunce zasu bai wa masu zanga-zanga kariya a Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

FB_IMG_1724055102512

'Yansanda sunce zasu bai wa masu zanga-zanga kariya a Katsina 

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayar da tabbacin cewa zata bada kariya ga masu zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 1 ga watan Oktiba.

Rundunar tace ta aiwatar damatakan da suka dace na ganin cewa zanga-zangar anyi ta cikin lumana. 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan tarzomar da ta barke a yayin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a fadin kasar a baya-bayan nan, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi na biliyoyin Naira.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ya shaida wa wakilinmu a Katsina a yammacin ranar Asabar da ta gabata cewa, rundunar ta kammala dukkanin shirye-shiryen ta na tabbatar da tsaro kafin zanga-zangar, da lokacin da kuma bayan ta.

Sadiq ya ce, “Mun dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.  An tura isassun ma’aikata don hana tabarbarewar doka da oda, tare da samar da bayanan sirri, sa ido, da sintiri a fadin jihar.

"Yayin da muka amince da 'yancin 'yan ƙasa na yin zanga-zangar, muna kira ga masu zanga-zangar da su yi amfani da waɗannan haƙƙoƙin cikin mutunci da bin tsarin doka."