Yan bindiga sun nemi sulhu da gwamnatin jihar Katsina

Yan bindiga sun nemi sulhu da gwamnatin jihar Katsina

Ƴan Ta'addar Daji Sun Bayyana Dalilin Dayasa Suka Kai Farmaki A Garin Maidabino

Yan bindiga sun nemi sulhu da gwamnatin jihar Katsina 

A wani faifan Bidiyo da ɓarayin dajin suka saki na tsawon Mintuna Tara da Sakan Hamsin da Bakwai ɓarayin sun baje kolin mutanen garin Maidabino da suka sace mafi akasarin su Mata da ƙananan Yara inda suke bayyana cewa ƴan Banga ne suka kashe masu matayen su shine suma suka shiga garin na Maidabino dake cikin ƙaramar hukumar Ɗanmusa inda sukayi awon gaba da waɗannan bayin Allah.

Kazalika sunyi barazanar cewa ita kanta ƙaramar hukumar Ɗanmusa a shirye suke zasu kai farmaki domin ɗaukar Mutane zuwa Daji nan bada Jimawa ba.

A bayanin su sun bayyana ƙarara yadda suke jin tsoron Ƴan Banga, sunce suna masu kisan wulakanci, sun kuma yi bugun gaban cewa Sojoji basu isa su zo su ƙwato waɗannan Mutanen da suke garkuwa dasu ba, kazalika ma gwamnan jihar Katsina.

Sun kuma nemi da ayi Sulhu dasu a cikin jawaban nasu, fatan da muke anan shine Allah ya bamu mahita daga wannan mummunan yanayin ta'addanci da muka tsinci kan mu a ciki. 

KU KARANTA KUMA: YAN BINDIGA SUN KASHE SHEHIN MALAMI A JAMI'AR FUDMA

Idan dai ba'a ban taba kimanin kusan Sati kenan da ɓarayin sukayi ƙwanton ɓauna da zummar farmakar ƴan kasuwar Maidabino akan hanyar su ta komawa gida lamarin da Jami'an tsaro suka hana, wanda sanadiyyar hakan ne ɓarayin dajin suka kai farmaki a Garin na Maidabino inda suka ƙone motoci shaguna Gidaje tare da awon gaba da Mutanen da suka ce sunfi Ɗari a hannun su.

Masu wannan harkar idan masu shiryiwa ne Allah ya shiryar dasu idan akasin hakan Allah bayin ka ne kai kasan yadda zakayi dasu.

Source: Source: Muhammad Aminu Kabir

Comment As:

Comment (0)