Wasu 'Yanbindiga Sun Yi Yunƙurin Shigowa Garin Katsina
Ɓarayin daji sun yi yunƙurin shigowa birnin Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Sunday, 18 Aug, 2024
Wasu 'Yanbindiga Sun Yi Yunƙurin Shigowa Garin Katsina
'Yanbindiga aƙalla su 50 sun yi yunƙurin shigowa birnin Katsina cikin duhun dare.
Shugaban 'Yanbanga a Katsina Alhaji Rabo, shi ne ya bayyana haka a ranar Asabar 17 ga watan Agustan 2024.
Ya ce, ɓarayin sun yi yunƙurin shigowa birnin jihar wajen ƙarfe 11:45 na dare, inda dakarun su na Filin Fayis Katsina suka samu rahoton sirri gameda fitowar 'Yanbindigar bi sa babura aƙalla su 50 daga wajen dazuzzukan Jibia da Batsari.
A cewar sa, ɓarayin sun aje baburan su a makarantar Tantagarya suka tako ƙasa zuwa gefen garin Babbar Ruga suka biyo ta gefen babban titin da ya zagaye birnin Katsina.
Tunda farko, ya ce, ɓarayin sun tsallako ta bayan bangon Jami'ar Umaru Musa Yar'adua, da jin labarin haka dakarun su na unguwar Shola, da ke Sabon Gida da Filin Fayis suka kwakkwanta ma su a wurare daban-daban.
Alhaji Rabo, ya nanata cewa, lokacin da 'Yanbindigar suka ga alamun an lura da su suka juya saboda sun tsorata sosai.
Haka kuma, ya shawarci sauran jamian tsaro su ci gaba da ayyuka tuƙuru domin ƙara ɗaukar ƙwararan matakan tsaro a wannan wuraren tun kafin su fara shigowa cikin Birnin Katsina.