Wani Mai Mota Ya Banke Jami'in KASROTA Har Lahira A Katsina
Jami'in KASROTA ya rasa ransa a lokacin gudanar da aiki a Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Thursday, 29 Aug, 2024
Wani Mai Mota Ya Banke Jami'in KASROTA Har Lahira A Katsina
An banke jami'in KASROTA har lahira a yankin ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Abubakar Marwana Kofar Sauri ya raba wa Manema Labarai a Katsina.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, a cewar sanarwar, Surajo Alhassan Dutsin-ma ya rasu ne bayan wata Mota ta banke shi a ƙaramar hukumar Kankia a lokacin da yake gudanar da aikinsa.
Majiyar ta ƙara da cewa, Gwamnan jihar ya bayyana alhininsa ga ma’aikatan hukumar ta KASROTA bisa rashin da hukumar ta yi, tare da addu’ar Allah ya baiwa iyalai da ‘yan uwan mamacin ikon jure rashisa.
Tun da farko, Dakta Dikko Umar Radda, ya miƙa ta’aziyyarsa ga hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Katsina (KASROTA) da ma’aikatar ayyuka ta jihar Katsina bi sa rashin ɗaya daga cikin ma’aikatan su Surajo Alhassan Dutsin-ma.
Marigayi Surajo Alhassan Dutsin-ma ya rasu ya bar Mata daya da ‘ya’ya huɗu Maza Biyu Mata Biyu.Tuni dai aka yi Sallar Jana'izarsa a garin Dutsin-ma kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.