Tsohon mataimakin gwamnan Katsina na PDP ya koma jam'iyyar APC
Hon. Surajo Umar Damari ya koma jam'iyyar APC
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Monday, 02 Sep, 2024
Tsohon mataimakin gwamnan Katsina na PDP ya koma jam'iyyar APC
Tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Katsina ya sauya sheƙa daga jami'ayyar PDP zuwa jam'iyyar APC
A ranar Lahadi 1 ga watan Satumba 2024, jam'iyyar APC a jihar Katsina ta yi babban kamu, inda tsohon mataimakin Gwamnan jihar, ya sauya sheƙa daga jami'ayyar adawa ta PDP zuwa jam'iyya mai mulki wato jam'iyyar APC.
Tsohon mataimakin Gwamnan Hon. Surajo Umar Damari, wanda ya yi ma tsohon Gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema mataimaki a wa'adin mulkin shi na farko, ya amshi katin shedar zama ɗan jam'iyyar APC bayan ficewa daga jam'iyyar PDP.
A lokacin da ya ba shi takardar shedar zama ɗan jam'iyyar APC a wajen taron jin ra'ayoyin al'umma da gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda Ph.D ya yi a shiyyar Funtua, mataimakin shugaban jam'iyyar Hon. Bala Abu Musawa.
Tun farkon, jawabinsa a wurin taron ya fara da ba 'yan jam'iyyar adawa da kuma iyayen ƙasa haƙuri a kan shiga al'amurran siyasa da yayi, duk da ba shi ne abinda ya tara al'umma a wajen ba, ya ƙara da cewa, amatsayinmu na 'yan siyasa duk inda mukaga wata ƙafa sai mu daɗe ta koda kaɗance don inganta siyasar su.