Shirin Dabarun Kula da Kanka Na DISC 2.0 Zai Bunƙasa Harkokin Kiwon lafiya A Jihar Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

Disc

Shirin Dibarun Kula da Kanka Na DISC 2.0 Zai Bunƙasa Harkokin Kiwon lafiya A Jihar Katsina 

Hanyar horas da Mutum yadda zai kula da kansa zata taimaka wajen inganta yanayin haihuwa tare da samar sakamako mai kyau a fannin kiwon lafiya. 

Haka tasa kungiyar kula da lafiyar iyali ta SFH haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina suka kaddamar da shirin Dibarun kula da kanka na shirin DISC 2.0 a ƙananan hukumomi 34 na jihar 

Wannan yunkuri zai maida hankali tare da karfafa harkokin kiwon lafiya ta hanyar dibarun kula da kanka a matsayin sake fasalin harkar kiwon lafiya tare da bada tabbacin ga iyalai a faɗin jihar Katsina musamman mata don ganin sun samu kyakkyawar kulawar a fannin kiwon lafiya 

An gudanar da wannan horo ne a ranar 17 zuwa 19 ga watan Oktoba, 2024 akan nuna kulawa da bada shawarari ga mata domin inganta shirin kula da ba da tazara wajen haihuwa a masaukin baki na Al-Hujrat, da ke Katsina 

Baban abinda wannan horo ya sanya gaba shi ne, ƙara samar da amince da ƙarfafawa a fannin kiwon lafiya domin koyar da mata samun kwarin gwiwa ta hanyar kauda duk wani tsoro a zukatan su, sannan su rungumi shirin kula da kanka wajen inganta tazarar haihuwa.

Haka kuma wannan horo ya kunshi bangaren auna fahimta da kuma na karatun keke-da-keke tare da karfafa mahimmanci amfani shawararin masana kiwon lafiya.

Bugu da ƙari shirin Dibarun kula da kanka na DISC 2.0 ya horas da jami'an kiwon lafiya daga ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina domin su bunƙasa ilmin akan batun samar da bayanai da rahotanni da ake samu daga cibiyoyin kiwon lafiya dangane shirin tazara wajen haihuwa a duk fadin jihar.

Da yake jawabi, shugaban hukumar kula da lafiyar al'umma a matakin farko, Dakta Shamsudeen Yahaya wanda ya samu wakilncin Dakta Shema'u Kabir Abba ta nuna farin cikin ta akan yadda hukumar kula da lafiyar iyali ta SFH wato Society for Family Health da shirin DISC 2.0 suka shirya wannan horaswa.

Dakta Shema'u Kabir Abba ta yi ƙarin haske akan mahimmancin samar da bayanai wanda ya zamo wani kalubale a hukumar kiwon lafiya ta jihar Katsina wanda take fatan cewa shirin DISC 2.0 zai ɗauki wannan batu da mahimmancin gaske ta hanyar samar da kayayyakin aikin da kuma horo domin magance matsalar.

" lallai wannan shiri zai taɓo mahimman wurare wanda nake da ammanar cewa wannan horo zai haifar da kyakkyawar sakamako wajen bunƙasa ɓangaren kiwon lafiya musamman a yankin ƙarkara wajen da ake da buƙatar haka fiye da ko'ina ' inji ta

Dakta Shema'u Kabir ta ƙara da cewa mahalarta wannan taro, ana sa ran za su yi amfani da ilimin da suka samu wajen koyar da ɗabi'ar nuna damuwa da bada shawarari ga bangaren kiwon lafiya fiye da 500 a ƙananan hukumomi 34 ta hanyar amfani da tunkarar mata a matakin farko.

Haka kuma ta ƙara da cewa wannan shiri na DISC 2.0 zai cigaba da share hanyan samar da da kyakkyawar yanayi da sakamako mai kyau a ɓangaren kiwon lafiya tare da bada gudunmawa mai karfi da zata farfaɗo da harkar kiwon lafiya.