An yi ƙarin girma ga jami'an NSCDC a Katsina Jami'an NSCDC 167 A Katsina Sun Samu Ƙarin Girma
Wednesday, 30 Oct 2024 00:00 am

Katsina Post

Jami'an NSCDC 167 A Katsina Sun Samu Ƙarin Girma

Wasu daga cikin jami'an hukumar tsaron NSCDC na Najeriya a Katsina sun samu ƙarin girma a matsayi daban-daban.

Daga cikin jerin waɗanda aka ƙara wa girman akwai mataimakan kwamandan hukumar (DCC) guda 6, mataimakan kwamandan II (ACC) guda 3, da PRO na hedikwatar da dai sauran muƙamai.

An taya waɗanda aka yi wa ƙarin girman murna, an kuma buƙace su da su ɗauki karramawar da akai masu a matsayin abinda zai ƙara masu ƙaimi wajen kara haɓɓaka ƙwazonsu na kare lafiya da dukiyar al’umar jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, an buƙaci jami’an na NSCDC a kan su kasance cikin shirin ko ta kwana don kare ƙasarsu a duk inda suke.

A lokacin da Katsina Post ta ziyarci gurin bikin ƙarin girman, an dai gudanar da bikin ƙarin girman a hedikwatar hukumar a ranar Talata, 29, ga watan Oktoba 2024.

A cikin jawabin kwamandan hukumar a Katsina, Jamilu Indabawa, ya buƙaci waɗanda aka yi wa ƙarin girman da su kasance masu ɗa a, ga al'umma kuma su ci gaba da yin aiki tuƙuru da kuma gujewa karɓar cin hanci da rashawa a yayin gudanar da ayyukan su na kare ƙasa.

Ya jaddada ma su cewa, dole su kasance masu ɗa a, da yin aiki tuƙuru don ɗaga martabar hukumar ko bayan ba ran su, tare da tsare lafiyar al’umar jihar Katsina da ma Nijeriya baki ɗaya.

A cewar sa, ƙarin girma da aka yi wa jami’an hukumar NSCDC ya tabbatar da ƙudurin babban kwamandan hukumar, Ahmed Abubakar Audi na inganta aikin jami’an.

Indabawa ya ce, tun da Abubakar Audi ya kama aiki a matsayin babban kwamandan hukumar ya duƙufa wajen inganta jin daɗin jami’an gami da sauya fasalin hukumar don inganta ayyukan su.