Gwamnatin Jihar Katsina tace a shirye take ta biya sabon tsarin albashi mafi ƙaranci na 70,000 da zaran Gwamnatin tarayya ta amince dashi.
Shugaban ma'aikatan Gwsmnatin Jihar, Alhaji Falalu Bawale yace Gwamna Dikko Raɗɗa ya shirya biyan sabon tsarin da zaran an kawo tsarin yanza za'a biya daga Gwamnatin Tarayya.
Shugaban Ma'aikatan da yake fira da manema labarai a ranar Jumma'a a ofishin sa ya bayyana ƙoƙarin da Gwamna Dikko Raɗɗa ke yi na kyautata ma Ma'aikata da ma waɗanda suka aje aiki a faɗin jihar.
Ya tabbatar da cewa Gwamna Raɗɗa zai cigaba da tsayawa tsayin daka wajen ganin anbiya haƙƙoƙin Ma'aikata.
Alhaji Falalu Bawale yace a satin daya gabata Gwamna ya bada kyautar motoci 4 da kuɗi miliyan 2 ga ma'aikata su 14 da sukayi zarra don ƙarfafa masu guiwa.
Daga nan ya tabbatar da cewa zuwa watan Dicemba Gwamnati zata kammala biyan kudaden giratuti na Maiakatan da suka rage a faɗin jihar.
Yayi albishir da yunkurin da Gwamnatin jiha keye ƙarƙashin jagoranci Malam Dikko Raɗɗa na biyan kudaden giratuti da zarar maaikaci ya aje aiki.