Ƙananan Hukumomin Katsina sun kashe Biliyan 128 a shekara Gwamnatin Katsina ta kashe Biliyan 128 ga ƙananan Hukumomi
Saturday, 20 Jul 2024 00:00 am

Katsina Post

Gwamnatin Katsina ta kashe Biliyan 128 ga ƙananan Hukumomi

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta kashe kimanin Naira Biliyan 128 ga ƙananan hukumomin jihar.

Majiyar ta tabbatar da cewa, bayanin gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin zaman majalisar zartarwa a fadar gwamnatin.

Tun da farko, ya ce asusun ƙananan hukumomin wani ɓangare ne na aiwatar da manufofi tare, kuma duk da fuskantar matsalolin tsaro da tattalin arziki, sun yi nasarar gudanar da ayyukan ci gaba a jihar.

A cikin jawabin gwamnan jihar, ya yi nuni da cewa gwamnatin ta na ci gaba da inganta ci gaban ƙananan hukumomin.

Haka kuma, a wani taron ‘yanmajalisar dokokin jihar, da ‘yanmajalisar zartarwa, da shugabannin ƙananan hukumomi, gwamnan ya bayyana cewa tsakanin watan Yunin 2023 zuwa watan Yunin 2024, kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta ware wa ƙananan hukumomin jihar ya kai kusan Naira biliyan Miliyan 130.1.

Ko a rahoton da Leadership ta rawaito, Gwamna Radda ya bayyana cewa an kashe Naira Biliyan 66 wajen biyan albashi, Naira biliyan 10.1 na fansho da giratuti, Naira biliyan 12.13 kan harkokin tsaro, da kuma Naira Miliyan 376.6 kan neman tsaro daga wasu ƙananan hukumomi. Sannan kuma an kashe Naira biliyan 4 wajen kashe kuɗaɗen gudanar da ayyuka kai tsaye ga ƙananan hukumomi.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa an ware Naira biliyan 15.1 don gudanar da ayyuka daban-daban daga ƙananan hukumomi, Naira miliyan 360 na kayayyakin koyarwa a makarantu, Naira biliyan 1.58 na tallafin karatu na ƙasashen waje da na cikin gida, da kuma Naira miliyan 939.8 don aikin Hajjin 2024.

Ya ƙara da cewa, an kashe Naira biliyan 6.14 wajen samar da Abinci, tare da karin Naira biliyan 3.1 na kayan aikin jinya da na salah da aka biya kai tsaye ga ma’aikatan kananan hukumomi da na karamar hukumar. An yi amfani da Naira biliyan 3.84 wajen siyan takin zamani, sannan an kashe Naira biliyan 1.19 wajen sayen kayayyakin amfanin Gona.

Kazalika, gwamnan ya amince da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na baya-bayan nan kan asusun hadin gwiwa na jihohi da ƙananan hukumomi. Ya bayyana damuwarsa gameda yadda hukuncin zai shafi biyan lamunin tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta fayyace komai a fili.

Gwamna Radda ya bayyana irin ƙoƙarin da jihar ke yi na magance matsalar rashin tsaro, da kafa hukumar sa'ido ta jihar Katsina, da kuma daƙile matsalar tsaro a ƙananan hukumomin dake fama da Iftila'in tsaro. Ya jaddada muhimmancin ci gaba da hada kai wajen yaki da rashin tsaro da ci gaban tattalin arziki.