Mutane 5 da za su iya maye gurbin Hon Tsauri a matsayin Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina

Mutane 5 da za su iya maye gurbin Hon Jabiru Tsauri a matsayin Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin j



Get Latest Updates - Sign Up for Our Newsletter

Name *
Email *
Phone *
Category *
Frequency *

Dikko

Mutane 5 da za su iya maye gurbin Hon Jabiru Tsauri a matsayin Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina 

Tun bayan da sanarwar sabon muƙamin da shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ba shugaban gidan gwamnatin jihar Katsina, Honorable Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri na ko'odinetan hukumar cigaban ƙasashen Africa watau New Partnership for Africa Development (NEPAD), al'ummar jihar suka zura ido su ga wa zai maye gurbin sa. 

Katsina Post ta yi duba na tsanaki a tsakanin wasu mutane biyar da ma su sharhi a kan al'amurran siyasar jihar suke ganin Gwamnan jihar zai iya ba mukamin na shugabancin ma'aikatan gidan gwamnatin jihar kuma ga su za mu zayyana:

1. Hon Abdullahi Turaji:

Yanzu haka dai Honorable Abdullahi Turaji shi ne Sakatare na musamman ga Gwamnan jihar Katsina watau Principal Private Secretary, PPS. 

Duk wanda ya san muhimmancin wannan mukamin to tabbas zai yadda da cewa Gwamnan zai iya maye gurbin Hon Jabiru Tsauri da shi musamman ma ana ganin ba bu ma su kusanci da Gwamnan a kamar mutanen biyu - watau Honorable Jabiru Tsauri da shi Hon Abdullahi Turaji. 

Haka zalika Honorable Abdullahi Turaji yana da ƙwarewa sosai ta aiki kuma yana daya daga cikin mutanen da suka san tsare-tsaren gwamnati da manufofin Gwamnan jihar domin suna tare da da Gwamnan tun kafin ma ya ayyana ra'ayin sa na tsayawa takara. 

2. Hon Musa Adamu:

Yanzu shi ne Kwamishinan Ma'aikatar Lafiya ta jihar Katsina kuma kafin nan ya riƙe mukamin Kwamishinan muhalli na jihar duk a karkashin jagorancin Gwamna Mallam Dikko Umar Radda. 

Sai dai kwarewa da iya aikin sa da kuma mu'amalar da mutane ta zarce haka domin ya taba wakiltar al'ummar karamar hukumar Funtua a majalisar dokoki kuma ya taba zama Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu da kuma ma'aikatar albarkatun Ruwa a gwamnatocin Barista Ibrahim Shema da kuma Rt Hon. Aminu Bello Masari a shekarun baya. 

A wani bangaren kuma, Honorable Musa Adamu Funtua shi ne ya jagoranci yaƙin neman zaɓen Dikko/Jobe a shiyyar Funtua lokacin yaƙin neman zaɓen 2023 da ya gabata. 

 

3. Dr. Kabir Magaji Gafiya:

Yanzu Dr. Kabir Magaji shi ne shugaban hukumar bayar da ilimin bai-daya ta jihar Katsina watau SUBEB kuma duk wanda ya san Gwamna Malam Dikko Radda to tabbas ya san irin amincin da ke tsakanin mutanen biyu domin bayanai sun tabbatar da cewa sun dade a tare. 

Haka zalika masana na ganin cewa zurfin ilimin sa da ƙwarewar sa da ma irin kyawawan riƙon da ya yi ma hukumar SUBEB na iya zama tsani gare shi wurin samun muƙamin na shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina. 

4. Hon Usman Abba Jaye:

Honorable Usman Abba Jaye dai yanzu shi ne Mai ba Gwamna Shawara kan harkokin masarautu. Amma kafin nan, ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Dutsin-ma.

Makusantan mutanen biyun sun tabbatar da kusancin su da karfin abotar su ba ma tun yanzu ba tun shekaru da dama da suka gabata kuma sun shaku sosai lokacin da dukkan su suna shugabancin ƙananan hukumomin su lokacin mulkin Marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua. 

Haka zalika ga wadanda suka bibiyi yadda Gwamnan jihar ta Katsina ya fara maganar takarar sa tun kafin ma ya samu tikitin jam'iyyar APC, ba zai yi mamaki ba idan har Gwamnan ya naɗa Honorable Usman Abba Jaye a matsayin sabon shugaban ma'aikatan gwamnatin sa. 

5. Alhaji Usman Isyaku:

Alhaji Usman Isyaku kwararren ma'aikacin gwamnati ne wanda ya aje aiki cikin shekarar nan bayan ya kai kololuwa inda ya riƙe shugaban ma'aikatan jihar Katsina. 

Yanzu haka dai Alhaji Usman Isyaku shi ne yake riƙe da muƙamin Mai ba Gwamna Shawara kan inganta ayyukan gwamnati watau Special Adviser to the Governor on Public Service Reform.

Ma su sharhi kan harkokin siyasa a jihar dai na ganin tabbas Gwamnan ya ji dadin aiki da shi lokacin da yana shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar wanda a lokacin sa ne gwamnati ta shirya ma manyan Sakatarori da daraktoci jarabawa tare da kawo wasu muhimman sauye-sauye a kan aikin gwamnati a faɗin jihar.

 

A cewar ma su sharhin, wannan ne ma ya sa gwamnan ya sake kirkirar wani sabon ofishin kan inganta ayyukan gwamnati kuma ya ba shi shugaban bangaren.

To, yanzu dai al'ummar jihar da dama sun zura ido domin su ga wa Gwamnan zai naɗa a sabon muƙamin na shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin.