Motar Tirela Ta Murƙushe Ƙurƙuƙura Da Fansinjoji A Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

PicsArt_03-03-08

Motar Tirela Ta Murƙushe Ƙurƙuƙura Da Fansinjoji A Katsina 

Babbar Mota ƙirar DAF ta tunguɗe Ƙurƙuƙura da fasinjojin dake ciki wanda duk akasarin su Mata.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar 02 ga watan Maris 2024 a kan titin Dutsin-ma kusa da Abdullahi Plaza a cikin birnin Katsina.

Kamar yadda shaidun gani da ido ya bayyana ma wakilin Katsina Post, yace yaron direban tirelar shi ne musabbabin faruwar lamarin, ya ce ga alamu kamar yaron tirelar bai ida gogewa da motar ba domin yana tada motar ta kubce masa ta nufo al'umma.

A cewar sa, da motar ta bangaji ƙurƙuƙurar sai ta tsallaka gudan tagwayen hannun ta nufi wata rumfa ta shige a ciki, yace gameda faruwar haɗarin ba a rasa rai ko ɗaya ba har a lokacin haɗa wannan rahoton.

Haka kuma, ya ƙara da cewa daga cikin fasinjojin Mata 5 ne da jariri 1 abin ya rutsa da su, saide Mace tsohuwa ɗaya ce kaɗai ta kare a cinyarta sai kuma jaririn da ya samu buguwa sosai.