Me ya sa Buhari bai je gaisuwar Hajiya Dada ba
Dalilin da ya sa tsohon Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari bai je gaisuwar Hajiya Dada ba
- Posted By: Mustapha Saddiq --
- Saturday, 07 Sep, 2024
Dalilin da ya sa tsohon Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari bai je gaisuwar Hajiya Dada ba
Tun bayan da labarin rasuwar Hajiya Dada, mahaifiyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ya bayyana, al'ummar Najeriya daga sassa daban daban suka fara yin tururuwa zuwa birnin Katsina domin yin ta'aziya ga iyalan Marigayiyar.
Dubban al'ummar ƙasar ne ma dai suka samu halartar jana'izar ta a ranar Talata a cikin ƙwaryar birnin na Katsina.
Sai dai jim kaɗan bayan kammala jana'izar ta ta, sai wasu mutane musamman a kafafen sadarwar zamani suka fara jefa alamar tambaya kan dalilin rashin ganin tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a wurin jana'izar da kuma zaman gaisuwa.
Wannan ne ya sa KATSINA POST ta binciki lamarin kuma ta tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar baya gida Najeriya.
A cewar majiyar mu wadda take kusa da tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya je birnin Landan na kasar Ingila domin a duba lafiyar sa.
"E, gaskiya ne, yanzu haka Tsohon Shugaban kasa yana Landan, yau (Asabar) satin sa uku da tafiya, shi ya sa ma ba'a gan shi ba.
"Amma ai mai magana da yawun sa, Garba Shehu ya fitar da sanarwar ta'aziyya zuwa ga iyalan Marigayiyar kuma da zaran ya dawo to zai je". In ji majiyar ta mu.