Majalisar Dokoki Ta Amince Da Dokar Wajabta Karatun Addini A Makarantun Boko A Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

Katsina State House of Assembly

Majalisar Dokoki Ta Amince Da Dokar Wajabta Karatun Addini A Makarantun Boko a Katsina 

Majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da kudirin dokar da ke wajabta karatun addini a duk makarantun firamare da sakandare da ke jihar.  

Yan'majalisar da suke tattaunawa aka dokar, sunce dokar zata taimaka wajen koyar da kyawawan ɗabi'u ga ƙananan yara ɗalibai.

Ƙudirin ya samu karɓuwa ne sakamakon wani rahoto da shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi, Hon. Mustapha Rabe Musa ya gabatar, wanda ‘yan majalisar suka amince da shi baki daya.  

Mataimakin kakakin majalisar, Rt. Hon. Abduljalal Haruna Runka, wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya umurci magatakardar majalisar da ya shirya daftarin doka na karshe domin mikawa Gwamna bisa amincewar sa.  

Idan aka sanya ma dokar hannu, za'a mayar Ilimin Addini a matsayin wani darasi na wajibi a dukkan makarantun firamare da sakandare na jihar Katsina.