Jami'an DSS sun kama jagororin zanga-zangar da aka gudanar a Katsina
Jami'an DSS sun kama jagororin zanga-zangar da aka gudanar a Katsina
- Posted By: Mustapha Saddiq --
- Friday, 02 Aug, 2024
Jami'an DSS sun kama jagororin zanga-zangar da aka gudanar a Katsina
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya watau DSS a jihar Katsina sun kama jagororin zanga-zangar da aka gudanar a garin Katsina.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, jami'an hukumar sun gayyaci mutane biyu daga cikin jagororin zanga-zangar zuwa ofishin su dake nan garin Katsina kuma daga bisani suka tsare su.
Wadanda suka gayyata din sun hada da Kabir Shehu Yandaki da kuma Habibu Ruma.
A cikin hotunan masu zanga-zangar Katsina da suka karade kafofin sadarwar zamani a jiya duka hadda mutanen biyu.
Daya daga cikin abokan wadanda aka kama wanda kuma ya bayyana ma Katsina Post cewa jami'an DSS din sun kira mutanen biyu ne ta waya da safiyar yau kuma suka bukaci su kai kan su ofishin su domin su ansa wasu tambayoyi game da zanga-zangar ta jiya.
KU KARANTA KUMA: AN SA DOKAR HANA FITA A KATSINA SABODA ZANGA-ZANGA
Sai dai a cewar sa, bayan sun je hedikwatar ta DSS dake Katsina sai jami'an suka tsare su.
Har ya zuwa yanzu lokacin hada rahoton dai ba'a saki mutanen ba.